Babban Kamu: FBI ta kwamuso wasu 'yan Najeriya da ke damfara a kasar Amurka
- Rahoto daga kasar Amurka ya bayyana yadda aka kwamushe wasu 'yan Najeriya da ke wa Amurka wa wayo
- Rahoton ya ce, an kame su ne da laifin aiwatar da damfara a cikin wani shirin gwamnati na tallafi
- An gano suna aikata wannan barka na kusan shekara guda; tun watan Oktoban 2020 zuwa Yuni na 2021
An cafke wasu 'yan Najeriya biyu a Amurka kan zargin damfara da sauran laifuka da suka kunshi dala dubu 25 kan kudaden tallafin da ake bai wa marasa aiki.
Jaridar Premium Times a rawaito cewa mutanen biyu da suka hada da Olushola Afolabi da Olugbeminiyi Aderibigbe ana zarginsu da damfarar ma'aikatar tsaron ma'aikata da gwamnatin Amurka ta shirin inshorar tallawa masara aikin yi.
An gano suna aiwatar da damfarar ne ta hanyar takardun shaidar bogi da suka kirkira wanda ke basu damar tura milyoyin daloli na tallafin marasa aiki zuwa wani asusun banki da suke kula da shi.
Wannan batu ya fito ne cikin wata takarda da gwamnatin Amurka ta gabatar kan wadanda ake zargin.
Ana zargin mutanen da aikata damfarar ne tsakanin watan Oktobar 2020 zuwa watan Yuni 2021.
Zargin Abba Kyari: An nada kwamitin mutum 4 da zasu binciki Kyari cikin makon nan
Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda (DCP), na iya bayyana a gaban kwamiti na musamman da ke binciken zarginsa da hannu a zambar intanet a wannan makon, jaridar Punch ta ruwaito.
Ku tuna cewa hukumar kula da ayyukan 'yan sanda (PSC) a ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta, ta dakatar da Kyari daga aiki kamar yadda sufeto janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba, ya shawarta a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli.
PSC ta bayyana cewa za a dakatar da Kyari har sai an kammala bincike kan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta yi, in ji jaridar The Nation.
Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya
A wani labarin daban, a yayin da aka dakatar da shugaban rundunar IRT, Abba Kyari, Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP) Alkali Baba Usman ya gargadi dukkan jami'an da kada su kuskura su zubar da mutuncinsu a idon jama'a.
Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Usman, ya yi wannan gargadin ne yayin kaddamar da ayyukan miliyoyin nairori da Olusoji Akinbayo, kwamandan runduna ta “B”, Apapa ya yi.
Shugaban 'yan sandan wanda ya samu wakilcin Johnson Kokumo, Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sanda (AIG) a sashen runduna ta 2 da ke jihar Legas, ya bayyana hakan ne a karshen mako.
Ya ce da zarar jami'i ya rasa goyon bayan jama'a to bai da wani dalilin da zai sadaukar da mutuncin ofishin sa.
Asali: Legit.ng