Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

  • Kungiyar matasan Arewa ta caccaki kotun Amurka da ya zargi Kyari da aikata cin hanci
  • Kungiyar ta ce hakan ba komai bane fa ce neman bata sunan jajirtattun jami'an Najeriya
  • Hakazalika, kungiyar ta ce tana nan daram za ta sanya ido kan abubuwan da ke faruwa

Jihar Kaduna: Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi kaca-kaca da Kotun Amurka da ke zargin Abba Kyari da cin hanci tare da bayar da umarnin cafke jami'in.

Sanarwar da shugaban AYCF na kasa, Yerima Shettima ya aikewa Legit.ng, ta bayyana umarnin a matsayin yunkurin tozarta jami'in dan sandan a cikin mahaifarsa kuma kasarsa mai zaman kanta.

Shettima, ya kuma yi gargadin cewa a tabbata abubu abin da zai faru da Kyari, inda ya bayyana matakin da FBI ta dauka a matsayin "abin da ba za a amince da shi ba, cin fuska ga 'yan kasarmu da izgili ga daya daga cikin manyan jami'anmu masu aiki tukuru."

Kara karanta wannan

Amurka ba ta da ikon kame Kyari, hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta yi martani

Matasan Arewa sun yi kaca-kaca da kotun Amurka kan Abba Kyari, sun yi kakkausan martani
Shugaban Kungiyar Matasan Arewa, AYCF | Hoto: Yerima Shettima
Asali: UGC

Babu wani dalilin da zai sa a gurfanar da Abba Kyari a Amurka

Kungiyar ta ce za ta ci gaba da bin diddigin abubuwan da ke faruwa a cikin lamarin, tare da jaddada cewa babu wata hujja da za a kebe daya daga cikin manyan 'yan sandan Najeriya mafi inganci da kokari a ci mutuncinsa.

A cikin sanarwar, kungiyar ta AYCF, ta bukaci dukkan 'yan Najeriya wadanda ke kishin kasa da gaske da su goyi bayan mutumin da yake aikin kasada don tabbatar da zaman lafiyar al'umma a kasar.

Ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da abin ya shafa a kasar, musamman kungiyoyin farar hula da su goyi bayan jami'in da ya yi kasadar rayuwarsa a ayyuka da dama a fadin Najeriya.

A cewarta, ayyukansa tuni an tabbatar da ingancinsu sau da yawa a kafafen watsa labarai na ciki da wajen Najeriya, ciki har da BBC.

"Duk da muna sane da ikon mallakarmu a matsayinmu na kasa, muna neman adalci ga mutumin da ke da bayanan da ba a iya kwatanta su ba a tarihin binciken Najeriya."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: IGP ya nemi a gaggauta dakatar da Abba Kyari daga aiki

Amurka ba ta ikon kame Kyari, hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta yi martani

A baya mun ruwaito cewa, Biyo bayan takaddamar da aka samu daga rahoton Amurka da ke tuhumar Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda (DSP), Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan sanda (PSC) a ranar Asabar, 31 ga Yuli ta yi martani kan takaddamar.

Vanguard ta ruwaito cewa hukumar ba ta sami rahoto na doka ba kuma mai ma'ana kan "bakon" zargin na Amurka mai umarnin kama Abba Kyari.

Legit.ng ta tattaro cewa PSC ta yi kira ga ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya da ya jagorance ta kan batun tunda ita (hukumar) ita ce hukumar da ke da ikon ladabtar da jami'an 'yan sanda da suka yi kuskure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel