Zargin Abba Kyari: An nada kwamitin mutum 4 da zasu binciki Kyari cikin makon nan

Zargin Abba Kyari: An nada kwamitin mutum 4 da zasu binciki Kyari cikin makon nan

  • Ana sa ran cikin makon nan ne kwamiti da zai binciki Abba Kyari bisa zargin cin hanci
  • Kwamitin a cewar rahotanni zai kunshi wasu manyan jami'an 'yan sanda kwararru na Najeriya
  • An zargi Abba Kyari da karbar cin hanci daga hannun wani dan damfara mai suna Hushpuppi

Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda (DCP), na iya bayyana a gaban kwamiti na musamman da ke binciken zarginsa da hannu a zambar intanet a wannan makon, jaridar Punch ta ruwaito.

Ku tuna cewa hukumar kula da ayyukan 'yan sanda (PSC) a ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta, ta dakatar da Kyari daga aiki kamar yadda sufeto janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba, ya shawarta a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli.

PSC ta bayyana cewa za a dakatar da Kyari har sai an kammala bincike kan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta yi, in ji jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

An dakatar da Abba Kyari daga aiki kan zargin hada kai da Hushpuppi, an fara bincikarsa

Abba Kyari da Hushpuppi: A makon nan kwamiti zai binciki Abba Kyari
Abba Kyari da Hushpuppi | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Wani shahararren dan damfara na intanet da ke fuskantar shari’a a Amurka, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya yi ikirarin cewa ya bai wa Kyari kudi don ya taimaka a cafke daya daga cikin ‘yan damfararsa a Najeriya.

Tuni dai Kyari ya musanta karbar wasu kudade daga Hushpuppi.

Kyari zai gurfana a gaban kwamitin manyan jami'ai hudu

Legit.ng ta tattaro cewa Kwamitin Bincike na Musamman wanda ya kunshi manyan jami'an 'yan sanda hudu, zai binciki zargin da ake yi wa Kyari.

Kwamitin zai kasance a karkashin jagorancin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda (DIG), Joseph Egbunike.

Hukumar 'yan sanda sun yi bayanin cewa ana sa ran dakatar da Kyari zai haifar da yanayin da zai ba kwamitin damar gudanar da aikin binciken ba tare da tsangwama ba.

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

A wani labarin daban, a yayin da aka dakatar da shugaban rundunar IRT, Abba Kyari, Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP) Alkali Baba Usman ya gargadi dukkan jami'an da kada su kuskura su zubar da mutuncinsu a idon jama'a.

Kara karanta wannan

Amurka ba ta da ikon kame Kyari, hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta yi martani

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Usman, ya yi wannan gargadin ne yayin kaddamar da ayyukan miliyoyin nairori da Olusoji Akinbayo, kwamandan runduna ta “B”, Apapa ya yi.

Shugaban 'yan sandan wanda ya samu wakilcin Johnson Kokumo, Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sanda (AIG) a sashen runduna ta 2 da ke jihar Legas, ya bayyana hakan ne a karshen mako.

Ya ce da zarar jami'i ya rasa goyon bayan jama'a to bai da wani dalilin da zai sadaukar da mutuncin ofishin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.