Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

  • Shugaban kasae Najeriya, Muhammadu Buhari, ya koma Abuja
  • Buhari ya garzaya Daura, bayan kaddamar da fara aikin layin dogo a Kano
  • Wannan shine karo na farko da zai je Daura tun bayan bullar cutar Korona

Bayan mako daya a mahaifarsa, Daura, jihar Katsina, shugaba Muhammadu Buhari ya ya koma birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuli, 2021.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa Buhari ya dira Abuja ne misalin karfe 5:40 na yamma.

A jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook, Malam Garba ya zayyana irin ayyukan da Buhari yayi daga Kano zuwa Daura a wannan lokaci.

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja
Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Yace:

Yayin ziyarar, shugaban kasa ya kaddamar da aikin ruwan Zobe, wanda zai samar da litan ruwa milyan 50 ga mutan jihar, hakazalika ya kaddamar da gidan gonar NALDA wanda zai samar da ayyukan yi ga jama'a."

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

"Bayan haka ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 50 na Dutsin-ma-Tsaskiya."

Ya kara da cewa gabanin komawarsa Abuja, Buhari ya karbi bakuncin Kakakin Majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, gwamnonin APC 12, mambobin majalisar dokokin jihar Katsina da sauran manyan jami'an gwamnati.

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

Mai martaba Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, ya ce Najeriya ta yi sa’a da samun Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa a irin wannan lokaci.

Basaraken ya ce abubuwa "da sun kasance da wahala matuka" idan da a ce ba Buhari ba ne yake jan ragamar mulkin kasar.

Ya yi magana ne a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli, lokacin da shugaban kasar ya ziyarce shi a fadarsa da ke Daura, jihar Kastina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel