An gina APC kan karairayi, bacin sunan jama'a, ba za ta wuce 2023, Lamido
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce APC ba zata kai labari a 2023 ba
- Tsohon ministan harkokin wajen yace an gina jam'iyyar APC da tubalin karya da yaudara ne
- Fitaccen dan siyasan yace barinsa jam'iyyar PDP tamkar cizon hannun da ya ciyar da shi ne
Dutse, Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Sule Lamido ya tuhumi tushen jam'iyyar APC inda yace jam'iyyar ba za ta wuce 2023.
Ya ce babu shakka APC zata rushe saboda an ginata ne da kiyayyar PDP inda ya kara da cewa ta kasa cika alkawurranta kuma an gano shugabanninta makaryata ne.
KU KARANTA: Gara in dinga samun N5 a Najeriya a kan in fita kasar waje: Budurwa ta bada labarin wahalarta a kasar waje
PDP za taa karba mulkin kasar nan a 2023
Tsohon ministan harkokin kasar wajen ya ce PDP za ta karba mulki a 2023 saboda 'yan Najeriya sun gaji da mulkin APC, Daily Trust ta ruwaito.
Sauya Sheƙa: Wasu Ƴan APC Sun Cinnawa Tsintsiyarsu Wuta, Sun Ce Suna Neman Mafaka a Ƙarƙashin Lemar PDP
A wata tattaunawa ta musamman da yayi da Daily Trust a ranar Lahadi, Lamido ya ce APC sun yi wa 'yan Najeriya dadin baki har suka yadda da cewa duk wani mugun abu a kasar nan ya fara ne daga PDP.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi nasarar cin zabe a 2015 bayan kamfen da aka yi na cewa za a shawo kan matsalar tsaron kasar nan, za a inganta tattalin arziki kuma a shawo kan rashawa. An sake zabensa a karo na biyu domin sake wasu shekaru hudu a 2019.
KU KARANTA: Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC da tayi zabukanta na gunduma, Tahir
Yadda jam'iyyar APC ke janye jama'a
Jam'iyyun hamayya ballantana PDP suna ta shirin zuwan zaben shugabancin kasa na 2023 yadda zasu fatattaki jam'iyyar mai mulki.
Tsohon gwamnan ya kara da kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabancin APC da bada kwarin guiwa ga 'yan sauran jam'iyyar domin komawa tasu. Yace suna amfani da bacin suna wurin samun mambobi.
A yadda Buhari ke karbar 'yan PDP a fadarsa, hakan bai dace ba. Wannan na nufin rashawa ne saboda satar ya'yan jam'iyya ita ce babbar rashawa," Lamido yace.
Ba zan taba komawa jam'iyyar APC ba
A kokarin janye shi zuwa jam'iyyar APC a 2014, Lamido yace kamar cizon yatsun da suka ciyar da shi ne.
Na ki zuwa ne saboda bana tsammanin suna da gaskiya. Kuma basu iya neman jama'a ba. A kan me zasu zageni kuma daga baya su zo suna fadin wani abu daban?
A cikin dukkan burikanmu da rabuwarmu a matsayin 'yan kasa, 'yan siyasa ko masu rajin karewa wasu hakki, mu fara duban kasarmu. Mu gina kasarmu ko kana APC ko PDP," yace.
Lamido yace bukatar gyara da ake yi ta taso ne saboda 'yan Najeriya sun sare kan shugabanci nagari, ganin rashin adalci yayi yawa da sauransu.
'Yan bindiga sun kutsa asibitin gwamnati a Zamfara
Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa babban asibiti gwamnati dake Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma'a.
Daily Trust ta tattaro cewa miyagun sun yi awon gaba da wata ma'aikaciyar jinya da kuma wata mai jinyar mara lafiya.
Mazauna yankin sun sanar da cewa bayan 'yan bindigan sun shiga asibitin, 'yan bindigan sun fara neman likita ko ma'aikatan jinya.
Asali: Legit.ng