Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC da tayi zabukanta na gunduma, Tahir

Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC da tayi zabukanta na gunduma, Tahir

  • Wani dan kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC, Mamman Tahir ya ce Antoni janar na kasa ya shawarcesu da su zabukan shugabannin jam'iyya na gundumomi
  • An tsara zaben ya kasance ranar Asabar amma ana tunanin ko dai kwamitin rikon kwarya da Mai Mala Buni yake shugabanta ta shirya ko akasin hakan
  • Sai dai a ranar Juma'a a Abuja Tahir yake tabbatarwa da manema labarai cewa a ranar 31 ga watan Yulin 2021 za a fara zabukan kamar yadda aka tsara

FCT, Abuja - Dan kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC, Mamman Tahir yace Antoni janar na kasarnan, Abubakar Malami ya shawarci 'yan jam'iyyar dasu fara zabukan gunduma.

An mayar da zabukan gundumomi na jam'iyyar APC ya kasance ranar Asabar, amma kuma akwai lauje cikin nadi, daya daga ciki shine ko dai kwamitin rikon kwarya wacce gwamna Mai Mala Buni su shirya taron ko akasin hakan.

KU KARANTA: Bartholomew Orr: Bidiyon Faston da ke tashi sama kamar tsuntsu, ya dira a coci don yin da'awa

Kara karanta wannan

Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC da tayi tarukanta, Tahir
Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC da tayi tarukanta, Tahir. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An dakatar da tarukan jihohi 3

Sai dai a ranar Juma'a a Abuja Tahir yace za a yi zabukan a ranar 31 ga watan Yulin 2021 kamar yadda aka shirya, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa an daga zabukan na jihar Kwara, Zamfara da Anambra zuwa wani lokacin na daban.

A cewarsa:

Saboda akwai zaben da za'ay i a Anambra kuma bama so mu samu matsala a can.A Zamfara kuwa har yanzu ana cigaba da rijistar 'yan jam'iyyar. Haka ne matsayarmu.
Ina so in sanar da kowa cewa tarukan jam'iyyarmu za su fara ne a ranar Asabar kuma kwamitin tana aiki da Antoni janar din kasar nan ne wanda ya bamu shawara kuma yanzu haka mun dauka.
Don haka komai zai cigaba da wanzuwa yadda ya dace. Muna so duk wasu 'yan jam'iyyar APC a kasar nan su fito su yi zaben gundumominsu.

Kotu ta dakatar amma zamu yi tarukan

Kara karanta wannan

Gwamna Buni Ya Yi Watsi da Hukuncin Kotun Koli, Ya Na Nan Daram a Shugaban APC

Tahir ya ce kotu bata riga ta bayyana matsayin kwamitocin ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kuma bamu san wanne hukunci zasu yanke ba kuma mun gamsu da matsayinmu a halin yanzu. Don haka muna shawartar duk wasu 'yan jam'iyyar da su fito su zabi wanda suke so don su tabbatar da zabinsu

KU KARANTA: Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

Duk yunkurin bata sunan Abba Kyari da mutuncinsa ba zai yi aiki ba, Fani Kayode

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya musanta zargin da ake yiwa DCP Abba Kyari bisa shiga cikin cakwakiyar amsar cin hanci daga hannun dan damfara Hushpuppi.

Kamar yadda rahotonni suka gabata, Abba Kyari yana da hannu a cikin wata harka wacce dan damfara Hushpuppi ya kaddamar a Dubai inda ya samu fiye da dala 20,000 akan harkar, TheCable ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel