Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki

Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki

  • Fitaccen mawakinnan Rick Ross yana da motoci na alfarma fiye da 100 amma bashi da lasisin tuki
  • Mawakin gambarar ya bayyana yadda yanzu haka yake cika takardun samun lasisin tukin
  • Ma’abota amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta mamakin yadda mai dukiya irinsa bashi da takardar tuki

Fitaccen Mawakin nan na gambara, Rick Ross yana da motocin alfarma guda 100 amma babban abin mamaki akansa shine bashi da takardar tuki.

Mawakin ya mallaki motocin wadanda duniya ke kallo tamkar taurari amma bai kware a tuki ba.

Rick Ross din wanda dan kasar Amurka ne ya shayar da ma’abota amfani da shafukan sada zumuntar zanani. Masoyansa sun yi matukar mamaki bayan bayyanar bidiyon mawakin wanda yake bayyana yadda yake da kasaitattun motocin amma sam bashi da takardar tabbacin ya iya tuki.

KU KARANTA: Bartholomew Orr: Bidiyon Faston da ke tashi sama kamar tsuntsu, ya dira a coci don yin da'awa

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki
Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki. Hoto daga @richforever
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

Ga bidiyon jerin motocin mawakin gambara Rick Ross:

Jama'a da dama sun dinga cece-kuce kan wannan al'amarin, inda suke ganin duk kudinsa da motocin da ya mallaka amma bashi da lasisin tuki.

Wasu suna ta tsokaci tare da nuna cewa basu yadda ba yayin da wasu suke mamakin rashin damuwarsa da abubuwan duniya.

DCP Abba Kyari: PDP ta ce bata son kumbuya-kumbuya, a bayyana komai

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci a zurfafa bincike akan DCP Abba Kyari bisa rahoton da FBI ta Amurka ta bayar akan hadin guiwarsa da rikakken dan damfarar yanar gizon nan, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, dama wata kotun Amurka dake California ta bukaci FBI ta bi sawun Kyari kuma ta gabatar dashi a Amurka bisa zarginsa da hada guiwa wurin yin damfarar miliyoyin daloli tare da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Bartholomew Orr: Bidiyon Faston da ke tashi sama kamar tsuntsu, ya dira a coci don yin da'awa

A wata takarda da kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya saki, ya bayyana yadda ake zargin Kyari da hannu dumu-dumu a damfarar a kasar ketare a matsayin babban abin kunya kuma abin Allah wadai da zubar da mutuncin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel