‘Dan uwan Abba Kyari ya yi maza ya goge hotunansa da motoci masu tsada a Instagram

‘Dan uwan Abba Kyari ya yi maza ya goge hotunansa da motoci masu tsada a Instagram

  • Usman Kyari ya goge duk wasu hotuna da bidiyoyin da ke shafinsa na Instagram
  • Matashin ‘dan uwan jami’in ‘dan sandan nan, Abba Kyari da aka taso gaba ne
  • Hakan na zuwa bayan sunan Kyari ya fito cikin badakalar Hushpuppi a Amurka

Najeriya- Usman Kyari, kanin babban jami’in ‘dan sandan Najeriya, DCP Abba Kyari ya goge hotunan da duk ya dauka a gefen wasu motoci masu tsada.

The Nation ta lura Usman Kyari ya shafe duk hotunan da ke shafinsa na Instagram ya na tunkaho da lumbutsa-lumbutsan motoci masu tsada na alfarma.

Ana zargin Usman Kyari ya goge hotunan da suke shafin sada zumuntan na sa ne a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli, 2021, bayan surutu sun fara yin yawa.

Jaridar ta ce har zuwa ranar Juma’a, Kyari mai mabiya fiye da 2, 000 a shafin Instagram bai goge wadannan hotuna na manya-manyan motoci da gidaje ba.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

Bayan rahotanni sun fara yawo cewa Abba Kyari na cikin wanda shahararren ‘dan 419 dinnan, Hushpuppi ya yi amfani da su, sai Usman ya cire hotunan.

Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi ya jefa DCP Abba Kyari a cikin matsalar da ta jawo hukumar FBI ta na neman ‘dan sandan a kasar Amurka.

‘Dan uwan Abba Kyari
Usman da Abba Kyari Hoto: www.globalgistng.com
Asali: UGC

Duk da Usman Kyari ya goge wadannan hotuna da ya dauka a baya, sai dai sun riga sun shiga Duniya.

A wasu daga cikin hotunan, za a ga ‘danuwan babban ‘dan sandan a gefen wasu manyan motoci kirar Jeep na Toyota SUV da kuma wata Mercedes Benz SUV.

Jaridar The Cable ta ce idan aka duba shafin @UsmanKyari_ a dandalin na Instagram a halin yanzu, za a ga cewa babu wani bidiyo ko hoto da aka wallafa.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Kyari ya bar wasu tsofaffin bidiyoyi a kafar Instastories, inda ‘danwansa Abba Kyari yake maida wa masu sukarsa martani.

Kara karanta wannan

Duk yunkurin bata sunan Abba Kyari da mutuncinsa ba zai yi aiki ba, Fani Kayode

Hushpuppi ya yi suna a dandalin Instagram

A baya kun ji gidan yari na jiran Hushpuppi bayan ya yarda bai da gaskiya da aka je kotu, ya na iya shafe shekaru 20 a kurkuku a dalilin barnar da ya yi.

Kafin ayi ram da Hushpuppi mai shekara 37, ya rika nuna wa Duniya dukiyar da ya tara. ‘Dan damfarar ya na da mabiya fiye da miliyan 2 a shafin Instagram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel