Duk yunkurin bata sunan Abba Kyari da mutuncinsa ba zai yi aiki ba, Fani Kayode
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya musanta amincewa da zargin Abba Kyari yana da hannu a damfarar da Amurka ke zarginsa dashi
- A cewar Fani-Kayode, koda jikinsa duk kunnuwa ne ba zai yarda da wannan zargin ba har sai ya ga kwakkwarar hujja akan hakan tukunna
- Yace Abba Kyari mutumin kirki ne wanda ya kware wurin kama ‘yan ta’adda fiye da kowanne jami’i a tarihi don haka shi ba zai amince da zargin nan ba
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya musanta zargin da ake yiwa DCP Abba Kyari bisa shiga cikin cakwakiyar amsar cin hanci daga hannun dan damfara Hushpuppi.
Kamar yadda rahotonni suka gabata, Abba Kyari yana da hannu a cikin wata harka wacce dan damfara Hushpuppi ya kaddamar a Dubai inda ya samu fiye da dala 20,000 akan harkar, TheCable ta wallafa
KU KARANTA: Nasara daga Allah: Danmaraki, Sama'ilo da wasu shugabannin 'yan bindiga sama da 20 na neman rangwame
An zargi Abba Kyari da taimakawa ta'addanci
Otis Wright na Amurka ya umarci FBI ta kama Kyari ko ya bayyana a California yayi bayani akan shigarsa damfarar $1,124,426.36.
A wata takardar kotu wacce Andrew John ya sanya hannu ya bayyana yadda Kyari ya hada kai da Hushpuppi wurin azabtar da dan uwan sana’arsa, Vincent Chinuzo don tabbatar da damfarar.
Sai dai Fani Kayode ya ce an shirya wannan tuggun ne musamman don a bata masa suna a idon duniya, Daily Nigerian ta wallafa.
Cikakkiyar takardar da Fani-Kayode ya wallafa
Jarumin da yake sadaukar da rayuwarsa wurin cetonmu daga hannun masu garkuwa da mutane da sauran azzalumai kuma ya kama masu laifi da dama fiye da kowanne jami’i za a ce ya amshi cin hanci a hannun wani dan damfara kuma a haka ake so mu yarda?
Abba gwarzo ne kuma yana da jarumta mai yawa don haka ba za mu yarda da zargin nan ba har sai an gabatar mana da kwararan hujjoji.
Mun yarda dashi fiye da tunanin mai tunani kuma bamu yarda da wani zargi da ake yi wa wannan mutum mai dunbin tarihin kama masu laifi ba.
‘Yan Najeriya suna kwasar nishadi idan aka zargi mafi kwazo a cikinsu. Wannan shine daya daga cikin matsalolinmu: muna jindadi mu yi murna idan aka zargi mutumin kirkin cikinmu da mafi munin laifi, sannan mu dauki karan tsana mu daura masa.
Ina rokon Abba da ya cigaba da ayyukansa na alkhairi kuma kada ya yarda ya mayar da hankalinsa akan wannan shirmen. An yi hakan ne musamman don a bata sunansa.
KU KARANTA: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 14, an damke masu kai musu bayanai 16, dabbobin sata 223
Buhari ya sha alwashin kara kasafin ilimi da kashi 50%
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin karin kasafin bangaren ilimi da kashi hamsin a cikin shekaru biyu masu zuwa, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Shugaban kasan ya sha wannan alwashin ne a wata takarda da ya saka hannu a gagarumin taron ilimi na duniya da yake halarta a yanzu haka a birnin London dake Ingila.
Mun mayar da hankali wurin karin kasafin kudi a fannin ilimi na kowacce shekara da kashi 50% a shekaru 2 masu zuwa kuma zamu kai 100% zuwa 2025, Shugaban kasan yace.
Asali: Legit.ng