An dakatar da Abba Kyari daga aiki kan zargin hada kai da Hushpuppi, an fara bincikarsa

An dakatar da Abba Kyari daga aiki kan zargin hada kai da Hushpuppi, an fara bincikarsa

  • Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda a Najeriya ta dakatar da Abba Kyari bisa zargin cin hanci
  • Wannan ya biyo bayan wani rahoto da cibiyar binciken Amurka ta FBI ta fitar kan Abba Kyari
  • Hukumar ta bayyana daga ranar da dakatarwar za ta fara aiki da kuma ranar da za ta kare

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban rundunar IRT daga gudanar da ayyuka da ayyukan ofishinsa, Vanguard ta ruwaito.

Wata sanarwa da Ikechukwu Ani, Babban jami'in Hulda da Jama'a ya ce:

"Dakatarwar Abba Kyari ta fara aiki daga ranar Asabar, 31 ga Yuli, 2021 kuma za ta ci gaba da jiran sakamakon bincike dangane da tuhumar da Ofishin Binciken Tarayyar Amurka ya yi.
“Hukumar ta kuma umarci Sufeto Janar na 'yan sanda da ya ba ta bayanai kan ci gaba kan lamarin don daukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

Yanzu-Yanzu: An dakatar da Abba Kyari daga aiki saboda zargin karbar cin hanci
Abba Kyari | Hoto: bbc.com
Asali: Twitter

Hukuncin hukumar na dauke ne cikin wata wasika mai lamba PSC/POL/D/153/vol/V/138 dauke da kwanan watan yau Lahadi, 1 ga watan Agustan 2021.

An zargi Abba Kyari da taimakawa Abbas Ramon wanda ake kira Hushpuppi, inda rahoton hukumar FBI ta kasar Amurka ta bayyana cewa, ya karbi cin hanci a hannun Hushpuppi.

Amurka ba ta ikon kame Kyari, hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta yi martani

Sai dai, kafin dakatarwar, Biyo bayan takaddamar da aka samu daga rahoton Amurka da ke tuhumar Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda (DSP), Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan sanda (PSC) a ranar Asabar, 31 ga Yuli ta yi martani kan takaddamar.

Vanguard ta ruwaito cewa hukumar ba ta sami rahoto na doka ba kuma mai ma'ana kan "bakon" zargin na Amurka mai umarnin kama Abba Kyari.

Legit.ng ta tattaro cewa PSC ta yi kira ga ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya da ya jagorance ta kan batun tunda ita (hukumar) ita ce hukumar da ke da ikon ladabtar da jami'an 'yan sanda da suka yi kuskure.

Kara karanta wannan

Amurka ba ta da ikon kame Kyari, hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta yi martani

IGP ya nemi a gaggauta dakatar da Abba Kyari daga aiki

A baya kadan, Sufeton 'Yan Sandan IGP Usman Alkali Baba, ya nemi a 'gaggauta' dakatar da Abba Kyari daga aiki bisa zargin karbar cin hanci da 'yan sandan Amurka ke yi masa kwanakin nan da ke da alaka da dan damfarar nan Abbas Roman Hushpuppi.

Baba, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Frank Mba ya fitar, ya ba da shawarar dakatar da Kyari nan take inda aka fara bincike akansa, in ji rahoton Daily Trust.

IGP ya kafa wani kwamati na mutum hudu karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike domin bincikar zargin da ake yi wa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta 'yan sanda wato IRT.

Asali: Legit.ng

Online view pixel