Babbar Magana: Jam'iyyar APC Ta Cire Kakakin Majalisar Dokoki Daga Wani Mukami
- Jam'iyyar APC a jihar Bauchi ta tumbuke kakakin majalisar dokoki daga mukamin shugaban masu ruwa da tsaki
- Kakakin majalisar, Hon. Abubakar Suleiman, ya yi watsi da wannan matakin na cire shi
- Yace jam'iyyarsa zata gudanar da tarukan unguwa don zaɓo shugabanni kamar yadda aka tsara
Bauchi:- Jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi ta sanar da cire kakakin majalisar dokokin jihar, Abubakar Suleiman, daga matsayin shugaban ƙungiyar masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Ningi, kamar yadda punch ta ruwaito.
Majalisar masu ruwa da tsakin ta haɗa da tsaffin yan majalisar tarayya da na jiha, tsaffin shugabannin karmar hukuma, jiga-jigan yan jam'iyya da kuma masu rike da muƙaman siyasa.
Sakateriyar APC ta ƙaramar hukumar Ningi tace an cire kakakin ne daga mukaminsa bayan samun umarnin hakan daga shugaban kwamitin riko na jiha.
Shin Hon. Suleiman ya amince da wannan matakin?
A ɓangarensa, Kakakin majalisar, wanda shine shugaban ƙungiyar shugabannin majalisun dokokin jihohin Najeriya, ya jaddada cewa har yanzun shine jagora a ƙaramar hukumar.
Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama
A wani jawabi da mai magana da yawunsa, Abdul Burra, ya fitar, yace ba zai yuwu a cire shi daga shugabancin masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Ningi ba.
Ya kuma roki masoyansa da su zauna lafiya da kowa kada su ɗauki doka a hannunsu.
Wani sashin jawabin yace:
"Har yanzun nine shugaban masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Ningi. Mafi yawancin yan majalisar suna tare da ni saboda haka ban amince da cire ni ba."
"Masu ruwa da tsakin ne ke da damar zaɓan shugabansu kuma ina da cikakken goyon bayan mafi yawan su in banda kaɗan."
"Zamu gudanar da zabukan unguwa da sauran waɗanda ke tafe kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyya ya tanazar."
A wani labarin kuma Gwamnatin Shugaba Buhari Zata Sake Kafa Dokar Kulle Saboda Sabuwar COVID19
Gwamnatin tarayya ta yi gargaɗin cewa Najeriya na gaf da faɗawa matsalar sake ɓarkewar annobar COVID19 a karo na uku a kwa nan kin nan.
Duk da an cigaba da bin dokokin kare yaɗuwar cutar amma an sami mutum 10 da suka harbu da sabon nau'in cutar da ake kira Delta COVID19.
Asali: Legit.ng