Gwamnatin Shugaba Buhari Zata Sake Kafa Dokar Kulle Saboda Sabuwar COVID19

Gwamnatin Shugaba Buhari Zata Sake Kafa Dokar Kulle Saboda Sabuwar COVID19

  • Gwamnatin tarayya ka iya sake kafa dokar kulle a kan yan Najeriya saboda ɓarkewar COVID19 karo na uku
  • Kwamitin yaki da cutar yace zuwa yanzun an gano aƙalla mutum 10 da suka kamu da sabon nau'in Delta COVID19
  • Sai dai ko da za'a sake kafa dokar kwamitin yace ba dukan ƙasa abun zai shafa ba

FCT Abuja:- Gwamnatin tarayya ta yi gargaɗin cewa Najeriya na gaf da faɗawa matsalar sake ɓarkewar annobar COVID19 a karo na uku a kwanankin nan.

Duk da an cigaba da bin dokokin kare yaɗuwar cutar amma an sami mutum 10 da suka harbu da sabon nau'in cutar da ake kira Delta COVID19.

Ɗaya daga cikin yan kwamitin yaki da cutar korona, Dr. Muktar Muhammed, yace a halin yanzun an fara duba yuwuwar sake kafa dokar kulle a wasu sassan ƙasar nan da abun ya fi muni.

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Gwamnatin Shugaba Buhari Zata Sake Kafa Dokar Kulle Saboda Sabuwar COVID19 Hoto: @buharisallau
Asali: Instagram

A jawabin Dr. Muhammed, yace:

"A gaskiya a kwanakin baya mun ga cewa annobar ta ja baya, domin ba a samun masu kamuwa da cutar sosai, amma yanzu yawan ya karu."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe

"Saboda mutane sun daina daukar matakan kariya, don haka ba abin mamaki ba ne idan yawan ya karu a yanzu."

Muhammed ya shaidawa BBC Hausa cewa a halin yanzun an gano mutun sama da 10 da suka kamu da sabuwar cutar Delta COVID19.

"Don haka lallai akwai wannan nau'i a Najeriya kuma yana karuwa, muna ma zargin cewa za a iya danganta karuwar masu kamuwa da cutar da shi wannan nau'i a yanzu haka." inji shi.

Sai dai a jawabin nasa ya bayyana cewa idan ma za'a sake kafa dokar kulle to sassan da abun yafi muni ne kadai dokar zata shafa ba kasa baki ɗaya ba.

Ya ake gane nau'in DELTA COVID19?

Ba wani sabon abu bane idan cuta ta hayayyafa da canza tsarin halittarta musamman a lokacin da take yaɗuwa sosai.

Kuma tun a bayana masana a fannin sun yi gargaɗin cewa sabbin nau'in cutar Korona ka iya bijirowa idan ba'a ɗauki mataki ba.

Kara karanta wannan

Kudin yin waya da hawa shafin yanar gizo zai karu a Najeriya, an kawo sababbin tsare-tsare

Duk da ba akai ga gano yadda yake yaɗuwa ba amma binciken masana ya nuna cewa sabon nau'in Delta yana da ƙarin hatsari fiye da na baya ta ɓangaren saurin yaɗuwarsa.

Tun a watan Mayun da ya gabata ne hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta kira sabon nau'in cutar a matsayin babban abin damuwa da ya kamata a mike tsaye.

Ko Delta COVID19 na haifar da wasu manyan cutuka masu zafi?

Har yanzun masana na kan bincike game da sabon nau'in cutar amma ga dukkan alamu Delta na haifar da wasu cutuka masu zafi da hatsari.

Wani mai bincike a Scotland ya gano cewa Delta yana hatsari sosai inda yace ya ninka nau'in Alpha ta wajen kasadar kwantar da wanda ya kamu da shi.

An gano cewa alamomin dake nuna mutun ya kamu da sabon nau'in korona wato Delta sun haɗa da, ciwon kai, bushewar makogwaro, majina da kuma zazzabi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

A wani labarin kuma Babu Wanda Zai Ci Nasara Fiye da Matakin Karatunsa, Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari , yace babu wani mutum da zai samu nasara fiye da ilimin karatun da yayi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Buhari ya bayyana cewa duk mutunin da yayi wasa ya rasa ilimi to ya rasa komai na rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel