Rudani a Kano bayan majalisar jiha ta gayyaci shugaban alkalai
- Wasikar gayyatar gaggawa da majalisar jihar Kano ta aikewa shugaban alkalan jihar ta baiwa jama'a mamaki
- An gano cewa majalisar ta gayyaci Mai shari'a Nura Sagir Umar kan hukuncin da babbar kotun jihar ta yanke
- Sai dai alkalin ya ki bayyana a gaban majalisar kuma NBA ta goya masa baya inda tace basu da wannan ikon
Kano - Wasikar gayyata da majalisar jihar Kano ta aikewa Mai shari'a Nura Sagir Umar, shugaban alkalan jihar Kano, ya kawo dimuwa a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
An tattaro cewa kwamitin a wasikar da daraktan shari'a Nasidi Aliyu yasa hannu mai kwanan wata 26 ga Yuli, ya bukaci babban alkalin da ya bayyana a gaban kwamitin a ranar 28 ga watan Yuli.
KU KARANTA: Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC da tayi zabukanta na gunduma, Tahir
Ko menene dalilin aikewa da wasikar?
An tattaro cewa an aike da wannan gayyatar ne saboda wani umarnin kotu da Mai shari'a Sanusi Ado Ma'aji ya bada na hana cigaba da bincikar dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar, Muhuyi Magaji Rimingado.
An gano cewa babban alkalin ya ki amsa gayyatar kuma bai yi martani ba balle ya bayyana a gaban kwamitin a ranar.
Mai magana da yawun fannin shari'a na jihar, Baba Jibo Ibrahim, ya sanar da manema labarai cewa sun yanke hukuncin mika lamarin ga kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano saboda basu son hada al'amura da mahukunta.
KU KARANTA: An gano makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara
Mun sha mamaki - NBA
A yayin da aka tuntubi shugaban NBA na jihar Kano, Aminu Gadanya, ya ce babban alkalin yayi daidai da bai bayyana a gaban kwamitin ba.
Ya ce:
Abun ya zo da bada mamaki. Na yi matukar mamaki da naji kwamitin majalisar jihar Kano ta gayyaci shugaban shari'a na jihar Kano.
Sun aike da gayyatar ranar Litinin kuma suke jiran shi a ranar Laraba. Na gano cewa makasudin gayyatar yana da alaka da wani umarni da alkalin babbar kotun jihar ya bada kan dakatar da majalisar.
Hushpuppi: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya gaya wa Buhari abin da ya kamata ya yi na mika Abba Kyari
NBA a matsayinta na kungiyar mai karfafa doka, bata amince da wannan gayyatar ba. Muna da ginshikai uku a gwamnati kuma kundun tsarin mulki ya bayyana aiki da karfin ikon kowannensu. So suke su fara tsorata fannin shari'a?"
Ya ce idan majalisar ta fusata da wani umarnin kotun, suna iya mika bukatar kawar da umarnin ko kuma su daukaka kara.
Babu daidai gayyatar shugaban shari'a. Ba su da hurumin gayyatar alkalin da ya bada wannan umarnin balle babban alkalin jihar. Don haka bamu amince ba. Mun sha mamaki da muka gane daya daga cikin mambobinmu ne yasa hannu kan wasikar," ya kara da cewa.
Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu
Rahotannin da Legit.ng ta fara tattarowa shine na fara shagalin bikin da daya tilo na shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar sarkin Bichi, Alhaji Nasir Bayero.
Kamar yadda shafin @insidearewa ya wallafa a daren ranar Juma'a, an ga hotunan amarya Zarah Bayero tare da angonta Yusuf yayin da ake gasar kwallon Polon bikinsu.
Wannan alama ce ta yadda aka fara shagalin bikin a ranar Juma'a duk da za a yi asalin daurin auren a farkon watan Augusta.
Asali: Legit.ng