Kudin yin waya da hawa shafin yanar gizo zai karu a Najeriya, an kawo sababbin tsare-tsare

Kudin yin waya da hawa shafin yanar gizo zai karu a Najeriya, an kawo sababbin tsare-tsare

  • Hukumar NCC ta kawo tsare-tsaren da za su jawo farashin yin waya ya karu
  • Kudin sayen ‘data’ domin hawa shafukan yanar gizo zai kara tsada a Najeriya
  • Umar Garba Danbatta ya bayyana cewa fasahar 5G ya kusa shigowa kasar nan

Abuja - Hukumar NCC mai kula da kamfanonin sadarwa na kasa suna yin wasu gyare-gyare da za su iya jawo farashin yin waya ya kara tsada a Najeriya.

Kamfanonin sadarwa za su kara biyan kudi

Daily Trust ta ce NCC za ta yi kwaskwarima a kan kudin AOL da ake karba a hannun kamfanonin sadarwa a duk shekara da kudin samun karfin yin waya.

NCC ta dauki wannan mataki ne ganin yanayin da ake ciki a halin yanzu, tare da samun karin kudin shigar da gwamnati ke samu domin bunkasa GDP.

Jaridar ta ce idan aka shigo da wannan sabon tsari, farashin yin waya da hawa yanar gizo a Najeriya zai karu.

Kara karanta wannan

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Shugaban hukumar NCC na kasa, Farfesa Umar Garba Danbatta, ya bayyana wannan da yake jawabi a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, 2021 a Abuja.

“Sauyin da aka kawo zai taimaka wajen karfafa kamfanonin sadarwa a Najeriya da tabbatar da cewa ana yi wa kowa adalci a kasuwannin Najeriya.”

Kudin yin waya da hawa shafin yanar gizo zai karu a Najeriya, an kawo sababbin tsare-tsare
Fasahar 5G Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Yunkurin farko da AOL zai yi shi ne a tabbatar da gyara lasisin da ake ba kamfanonin sadarwan.

Shugaban na NCC ya ce hukumar ta dogara da sashe na 21 na dokar NCA da aka kafa a shekarar 2003 wajen wannan karin farashi da za ayi wa kamfanonin.

Za a shigo da fasahar 5G Najeriya - NCC

“Bayan haka, hukumar NCC ta fara kokarin kawo fasahar 5G a Najeriya. Nasarar shigo da wannan fasaha a Najeriya ya dogara ne da sauyin da za a kawo.”

Farfesa Umar Garba Danbatta ya bayyana cewa nan ba da dade wa ba za a ga 5G a kasar nan, ya ce sauran kasashen Duniya ba za su bar Najeriya a baya.

Kara karanta wannan

Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari

A kwanakin baya ne shugaban hukumar NCC mai kula da sadarwa, Farfesa Umar Danbatta, ya ce ma’aikatar sadarwa ta na shirin rage farashin ‘data’.

NCC ta bayyana haka ne a lokacin da shugabanta ya yi magana da ‘yan jarida a Kano. NCC ta ce su na kokarin rage kusan 60% na kudin hawa yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng