Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kwamushe Tsohon Gwamnan Kwara da Zargin Karkatar da Kudi

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kwamushe Tsohon Gwamnan Kwara da Zargin Karkatar da Kudi

- Hukumar EFCC ta yi babban kamu yayin da ta kame tsohon gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed

- Rahoto ya bayyana cewa, ana zargin gwamnan da karkatar da wasu makudan kudade mallakar jihar

- An tsare tsohon gwamnan na tsawon awanni bakwai yayin da yake ba da bayanai kan kudaden

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.

Wasu majiyoyi a hukumar sun fada wa gidan Talabijin na Channels cewa wasu gungun ma’aikata ne suka gurfanar da tsohon gwamnan a hedkwatar EFCC da ke yankin Jabi a Abuja, babban birnin kasar.

An ce ya isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar Litinin, a kan amsa gayyatar da hukumar ta yi masa.

KU KARANTA: Wakilin Birnin Bauchi: Gwamnan Bauchi Ne Ya Kitsa Yadda Aka Dakatar Dani

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kwamushe Tsohon Gwamna da Zargin Sama da Fadi
Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kwamushe Tsohon Gwamna da Zargin Sama da Fadi Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Bayan isowarsa ofishin hukumar ta EFCC, Mista Ahmed ya kasance a dakin bincike na kimanin awanni bakwai, yana bada bayanai.

Duk da cewa ba a samu cikakkun bayanai ba, majiyoyi sun bayyana cewa kamun nasa na da nasaba da yadda aka karkatar da wasu kudade har kimanin Naira biliyan 9 daga asusun gwamnatin jihar Kwara.

An yi zargin cewa an karkatar da kudin a lokacin Mista Ahmed da yake gwamnan jihar, da kuma lokacin da ya yi Kwamishinan Kudi a gwamnatin tsohon gwamna Bukola Saraki.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan ya amsa gayyatar hukumar.

Amma, ya ki karin bayani.

KU KARANTA: Gwamnoni 13 Na PDP Sun Shiga Taron Sirri Don Tattauna Matsalar Rashin Tsaro

A wani labarin, A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo ta ba da sanarwar cewa ta cafke wani dan sanda na bogi kuma dan bindiga, mai suna Michael Osundu.

A cewar kakakin rundunar, tare da Orlando Ikeokwu, an gano bindiga guda daya da harsasai 26, da kuma kakin ‘yan sanda guda biyu masu mukamin Mataimakin Sufeta Janar, wadanda aka boye su a cikin motarsa ​​kirar Toyota Escalade mai bakin gilashi.

Ikeokwu ya bayyana cewa ana zargin Osundu dan kungiyar 'yan daba ne da suka kai hari hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar da kuma gidan yari na Owerri a ranar 5 ga Afrilu, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel