Gwamna Masari na Katsina ya bayyana mafita ga matsalar rashin tsaron Najeriya

Gwamna Masari na Katsina ya bayyana mafita ga matsalar rashin tsaron Najeriya

  • Gwamnan jihar Katsina ya bukaci masu ruwa da tsaki da su zuba hannun jari kan matasa
  • Ya bayyana hakan ne a matsayin mafita ga yawaitar aikata laifuka da kasar nan ke fuskanta
  • Gwamnan ya ce zuba jarin ne hanya mafi sauki domin dakile matasa daga aikata munanan ayyuka

Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina, ya ce ilimi na iya zama maganin 'yan ta'adda dake addabar kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya yi kira da a sanya hannun jari mai yawa ga ilimtar da matasa da ci gaba a matsayin wata hanya ta magance rashin tsaro a Najeriya.

Masari ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da Ibrahim Musa-Kalla, sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar, ya fitar a ranar Lahadi, 24 ga watan Yuli, 2021.

Gwamna Masari na Katsina ya bayyana mafita ga matsalar rashin tsaron Najeriya
Gwmnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A cewar gwamnan, sanya hannun jari a harkar ilimi zai samar da dama ga matasa su kasance masu manufa a maimakon tsunduma wa cikin tashin hankali da aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Ba aikin mu bane dakatar da masu fafutuka , sai dai ba za mu laminci rikici ba - Rundunar Sojoji

A cewarsa:

"Dukanmu muna da alhaki kan tabbatar da cewa al'ummarmu tana cikin aminci, muna bukatar masu ruwa da tsaki su zuba jari a cikin mutane."
"Ana bukatar kungiyoyi, attajirai da kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da su sanya hannu jari kan wannan."

Masari ya ce sahihiyar sanya hannun jari ga ci gaban matasa da ilimi ne zai taimaka wa matasa su bi hanyar da ta dace.

Ya kara da cewa:

“Ta hanyar ilimantar da matasan mu, zamu rage 'yan bindiga. Ka zabi wani a yankinku ka tura shi makaranta domin taimakawa al'umma."

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

Wani matashi dan shekaru 35 da ke neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar Kano, Malam Aminu Sa’idu, a jiya ya gana da mataimaka na musamman (SAs) ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje don sanar da su burinsa.

Kara karanta wannan

Sarki a arewacin Najeriya ya ba Fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 su bar jiharsa

Da yake magana da Daily Trust bayan ganawar, matashin ya ce yana daga cikin shawarwarin da yake bi gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Ya kuma ce ganawar ta yi daidai da kudirin dake rajin ba matasa damar a dama dasu a mulki na"Not Too Young to Run", da kuma dabarun fadada aniyarsa zuwa dukkan sassan kasar.

Minista Lai Mohammed ya magantu kan matsalolin kabilanci da addini a Najeriya

A wani labarin, Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce wasu mutane a Najeriya na kokarin wargaza kasar saboda dalilai na son kai.

Premium Times ta ruwaito cewa Mohammed yayi wannan bayani ne a ranar Asabar, 24 ga watan Yuli, a Abuja a taron gabatar da wani littafi.

Ya yi zargin cewa wasu abubuwa na kokarin kara tabarbarewar rikicin kabilanci da bambancin addini a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel