An gano makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara

An gano makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara

  • Fitaccen dan kwallon kafan Najeriya, Ahmed Musa ya samu wurin zama a sabuwar kungiyar kwallon kafa da ya koma
  • Dan kwallon kafan mai shekaru 28 ya koma wata kungiyar kwallon kafa a kasar Turkiyya kuma zai dinga samun N1bn a kowacce shekara
  • Kungiyar kwallon kafan ta kasar Turkiyyan ta saka buri kan sabon zakaran da ta samu a wasannin nan gaba

Istanbul, Turkiyya - Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya sa hannu kan wata sabuwar harkalla da wata kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya bayan kwashe watanni hudu da Kano Pillars.

Kamar yadda Legit.ng ta gano, kungiyar kwallon kafan ta gabatar da matashin zakaran mai shekaru 28 a duniya bayan an yi masa gwajin lafiya.

KU KARANTA: Dalla-dalla: Shin da gaske 'yan Boko Haram na shigo da motocin yaki ta iyakokin Najeriya?

An gano makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara
An gano makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara. Hoto daga Ulrik Pedersen/NurPhoto
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Bartholomew Orr: Bidiyon Faston da ke tashi sama kamar tsuntsu, ya dira a coci don yin da'awa

Kara karanta wannan

Kudin yin waya da hawa shafin yanar gizo zai karu a Najeriya, an kawo sababbin tsare-tsare

Babu shakka wannan makuden kudaden ne suka saka zakaran kwallon kafan ya kasance daya daga cikin 'yan kwallon kafa da yafi kowa samun kudi a duniya.

Fitaccen dan wasan kwallon kafan ya shiga tsararrakinsa a yayin da yake kokarin farfadowa yayin da a bangaren Super Lig kuwa suke ta shirye-shiryen wasannin 2021-22.

Ya bar kungiyar Al Nassr a shekarar da ta gabata

Kafin komawarsa Turai, Musa ya bar kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr dake Saudi Arabia a watan Oktoban da ya gabata kuma yayi yunkurin komawa kungiyar West Bromwich Albion a watan Janairun da ta gabata amma hakan ya gagara.

Marwa ya bukaci jami'an NDLEA da aka yi wa karin girma da su mutsike masu safarar kwayoyi

Buba Marwa, shugaban NDLEA ya umarci jami’an tsaro da su ragargaji masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Marwa ya yi wannan maganar a ranar Laraba yayin wani taro na kara wa manyan jami'an NDLEA girma a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

Buhari ya sha alwashin kara kasafin ilimi da kashi 50% a cikin shekaru 2

A cewarsa wannan salo ne na musamman na yaki da harkar miyagun kwayoyi a kasar nan kuma hakan da alamu zai cimma nasara, TheCable ta ruwaito.

Wannan yaki ne wanda wajibi a dage akan shi, gaba daya sai an bincike kasar nan kuma zamu samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: