Dalla-dalla: Shin da gaske 'yan Boko Haram na shigo da motocin yaki ta iyakokin Najeriya?
- A ranar Asabar wani IUnit68 ya wallafa a shafinsa na Twitter inda yace ‘yan Boko Haram suna shigo da makamai ta iyakokin kasa
- Wanda yayi wallafar yace ya yi mamaki akan yadda akabar motocin cike da miyagun makamai suke shigowa kasar nan har zuwa Sambisa
- A cewarsa akwai babbar ayar tambaya akan yadda ake shigowa da makamai kasar nan kuma har suke kaiwa ga ‘yan boko haram
A ranar Asabar da ta gabata ne wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ya bayyana yadda ‘yan Boko Haram suka shigo da motoci 6 cike da miyagun makamai kuma suka ratsa dashi cikin kasar nan.
Mutumin mai amfani da suna IUnit68 ya sanya alamar tambaya akan yadda ake shigowa da miyagun makamai ta iyakokin kasa har a kai su dajin Sambisa a mika su ga ‘yan ta’adda.
KU KARANTA: Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna
Bayan wallafar ya sanya hoton motocin masu cike da miyagun makaman.
Wallafar ta janyo cece-kuce inda mutane da dama suka yi ta tofa albarkacin bakunansu.
Kamar yadda ya wallafa:
Boko Haram sun shigo da wasu motoci cike da makamai. Kwanan nan suka shigo da motoci da aka ratso dasu ta iyayokin kasa kuma an shigar dasu Sambisa don Boko Haram su cigaba da ta’addanci suna addabar al’umma.
KU KARANTA: Ango dake aiki kan na'ura mai kwakwalwa yayin bikinsa ya janyo cece-kuce
Shin akwai gaskiya a wannan wallafar?
Sunan mawallafin Western Media kuma akwai hoton Nnamdi Kanu a shafinsa. An gano cewa da yawa daga cikin wallafar dake shafinsa ba tashi bace, sake wallafa su yayi kuma sun fi alaka da kungiyar IPOB.
Karin binciken da thecable tayi yasa an gano cewa ana amfani da shafin ne domin yada farfaganda da karya ga jama'a.
Wallafar bata bayyana ranar da aka shigo da ababen hawan ba. Bincike kan hoton ya nuna cewa an fara wallafa su ne a Shutterstock, New York, Amurka. Hakan yana nuna cewa ababen hawan ba na Boko Haram bane.
Hukunci
Ikirarin cewa Boko Haram ne suka shigo da ababen hawan yakin shida ta iyakokin Najeriya duk karya ne kuma an yi hakan ne domin yada farfaganda.
Hoton ababen hawan na dakarun sojin Lithuania ne ba na Boko Haram ba.
'Yan bindiga sun sako sarkin Jaba
Miyagun 'yan bindiga sun sako babban basaraken jihar Kaduna, Danladi Gyet Maude, wanda aka sace a jihar Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.
Legit.ng ta ruwaito muku yadda aka sace basaraken a ranar Litinin yayin da yaje duba gonarsa dake Panda a jihar Nasarawa.
Amma wata majiya daga fadar ta sanar da Daily Trust cewa an sako basaraken a ranar Laraba wurin karfe tara da rabi na dare. Sai dai majiyar bata bayyana cewa an biya kudin fansa ba ko ba a biya ba.
Asali: Legit.ng