Bartholomew Orr: Bidiyon Faston da ke tashi sama kamar tsuntsu, ya dira a coci don yin da'awa

Bartholomew Orr: Bidiyon Faston da ke tashi sama kamar tsuntsu, ya dira a coci don yin da'awa

  • Ko wanne fasto yana da nashi salon na daban na janyo hankalin mabiyansa yadda zasu kara imani dashi
  • Hakika wani fasto dan Amurka ya zo da nashi salon na musamman wanda ya nishadantar da jama’a da dama
  • Fasto Bartholomew ya isa coci da tamkar tsuntsu inda aka ga ya dira coci tare da bayyana domin fara da'awah

Batholomew Orr - Bayyanar bidiyon wani fasto dan Amurka wanda yake tashi sama tamkar tsuntsu mai fiffike ya nishadantar da jama’a da dama.

Bidiyon wanda faston ya wallafa a Youtube yana tashi sama yayin da ya tara jama’a a majama’a ya janyo cece-kuce.

KU KARANTA: Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna

Bartholomew Orr: Bidiyon Faston da ke tashi sama kamar tsuntsu, ya dira a coci don yin da'awa
Bartholomew Orr: Bidiyon Faston da ke tashi sama kamar tsuntsu, ya dira a coci don yin da'awa. Hoto daga dailymail.co.uk
Asali: UGC

Wannan tashin na faston ya baiwa wasu da dama dariya yayin da wasu suka yi ta al’ajabin irin wannan baiwa da faston yake da ita. Dama a wani taro da faston ya taba yi a 2018 ya sanar da ‘yan cocin cewa Jesus yana nan dawowa a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje Ta Maida Martani Kan Shirin Hana Mata Tukin Mota a Ƙano

Fasto Batholomew yace mu'ujizar Ubangiji ce ke rike da shi

Faston mai suna Bartholomew Orr na cocin Brown Missionary dake Southaven a Mississippi a Amurka ya zama sanannen mutum cikin kankanin lokaci.

Kamar yadda ya tabbatar wa mabiyansa, bai san lokacin da yake tashi sama ba kuma ga dukkan alamu Ubangiji ne yake so ya nuna wata aya shiyasa ya bashi ikon tashi a sama.

Sannan ya ce yana matukar jindadin yadda yake wa’azi a sama yayin da wani abu yake rike dashi, Daily Mail ta wallafa.

KU KARANTA: Ango dake aiki kan na'ura mai kwakwalwa yayin bikinsa ya janyo cece-kuce

Manyan 'yan bindiga sama da ashirin na neman rangwame

Sakamakon ruwan bama-baman da ‘yan bindiga suke jefawa dajikan da suke jihohin arewa maso yamma da arewa ta tsakiyan kasar nan, 'yan bindiga sun fara laushi suna zubar da makamansu.

Kamar yadda Daily Nigerian ta bayyana yadda wasu manyan takadaran ‘yan bindiga suka fara mika wuya suna zubar da makamansu.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Shin da gaske 'yan Boko Haram na shigo da motocin yaki ta iyakokin Najeriya?

Kamar yadda jami’in ya tabbatar:

Wasu daga cikin shugabannin ‘yan bindiga fiye da 20 da sauran shugabannin ‘yan ta’addan sun fara lallabawa cikin sirri suna rokon jami’an tsaro yafiya da kuma sassauci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel