DCP Abba Kyari: PDP ta ce bata son kumbuya-kumbuya, a bayyana komai

DCP Abba Kyari: PDP ta ce bata son kumbuya-kumbuya, a bayyana komai

  • Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci Najeriya ta zurfafa bincike akan rahoton da FBI ta Amurka ta bayar akan alakar DCP Abba Kyari da Hushpuppi
  • Dama FBI ta bukaci a gabatar mata da Abba Kyari bisa zarginsa da hada guiwa da Hushpuppi wurin yin damfarar miliyoyin daloli
  • Sanin kowa ne cewa Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi rikakken dan damfarar yanar gizo ne, don haka akwai alamar tambaya akan lamarin

FCT, Abuja - Jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci a zurfafa bincike akan DCP Abba Kyari bisa rahoton da FBI ta Amurka ta bayar akan hadin guiwarsa da rikakken dan damfarar yanar gizon nan, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, dama wata kotun Amurka dake California ta bukaci FBI ta bi sawun Kyari kuma ta gabatar dashi a Amurka bisa zarginsa da hada guiwa wurin yin damfarar miliyoyin daloli tare da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Duk yunkurin bata sunan Abba Kyari da mutuncinsa ba zai yi aiki ba, Fani Kayode

KU KARANTA: Buhari ya sha alwashin kara kasafin ilimi da kashi 50% a cikin shekaru 2

DCP Abba Kyari: PDP ta ce bata son kumbuya-kumbuya, a bayyana komai
DCP Abba Kyari: PDP ta ce bata son kumbuya-kumbuya, a bayyana komai. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Abun kunya da na Allah wadai ne

A wata takarda da kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya saki, ya bayyana yadda ake zargin Kyari da hannu dumu-dumu a damfarar a kasar ketare a matsayin babban abin kunya kuma abin Allah wadai da zubar da mutuncin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Cikakkiyar takardar da PDP ta fitar

Hakika wannan zubar da kimar kasarmu ne kasancewar babban mutum mai rike da kujera mai daraja a mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bige da damfara a kasar ketare.
Jam’iyyarmu tana bukatar kada a boye wannan al’amarin kuma a yi bincike mai zurfi akan Kyari da wasu manyan masu shugabanci a karkashin jam’iyyar APC.
Muna rokon shugaba Buhari akan kada ya sassauta yayi gaggawar dawo da mutunci da darajar kasar nan kuma ya bari a yi bincike mai zurfi akan wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke 'yan bindiga 14, an damke masu kai musu bayanai 16, dabbobin sata 223

Sannan matukar ba a kawo garambawul akan wannan matsalar ta Abba Kyari ba, bacin sunane ga ‘yan sandanmu, harkokin tsaronmu da kasarmu baki daya.
Don haka PDP tana bukatar Buhari da ya mika Abba kyari hannun IGP don a yi bincike a kansa kuma matsawar aka tabbatar da zargin da ake masa gaskiyane to a yi gaggawar mika shi ga FBI, kamar yadda takardar tazo.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Danmaraki, Sama'ilo da wasu shugabannin 'yan bindiga sama da 20 na neman rangwame

'Yan bindiga sun sako Sarkin Jaba

Miyagun 'yan bindiga sun sako babban basaraken jihar Kaduna, Danladi Gyet Maude, wanda aka sace a jihar Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito muku yadda aka sace basaraken a ranar Litinin yayin da yaje duba gonarsa dake Panda a jihar Nasarawa.

Amma wata majiya daga fadar ta sanar da Daily Trust cewa an sako basaraken a ranar Laraba wurin karfe tara da rabi na dare.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Amurka Ta Bada Umurnin a Kamo Mata DCP Abba Kyari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng