'Yan bindiga sun sako babban basaraken Kaduna da suka sace

'Yan bindiga sun sako babban basaraken Kaduna da suka sace

  • Miyagun masu garkuwa da mutane sun sako Sarkin Jaba, Danladi Gyet Maude wanda aka sace a ranar Litinin
  • An gano cewa sun sako shi a daren Laraba wurin karfe tara da rabi na dare inda aka gan shi a fadarsa tare da mabiyansa
  • Babban basaraken mai daraja ta daya yadade yana rike da sarautar Jaba kuma yana daga cikin tsoffin sarakuna a jihar

Miyagun 'yan bindiga sun sako babban basaraken jihar Kaduna, Danladi Gyet Maude, wanda aka sace a jihar Nasarawa a ranar Litinin da ta gabata, Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito muku yadda aka sace basaraken a ranar Litinin yayin da yaje duba gonarsa dake Panda a jihar Nasarawa.

KU KARANTA: Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya

'Yan bindiga sun sako babban basaraken Kaduna da suka sace
'Yan bindiga sun sako babban basaraken Kaduna da suka sace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC ta daskarar da asusun bankin 'yar majalisa bayan ta siya motar N1bn

An sako Gyet Maude a daren Laraba

Kara karanta wannan

El-Rufai ya sanar da abinda suke yi da gwamnatin Nasarawa wurin ceto basaraken jiharsa

Amma wata majiya daga fadar ta sanar da Daily Trust cewa an sako basaraken a ranar Laraba wurin karfe tara da rabi na dare.

Sai dai majiyar bata bayyana cewa an biya kudin fansa ba ko ba a biya ba.

Tsohon basaraken mai shekaru tamanin da uku a duniya an sako shi bayan sa'o'i arba'in da takwas da sace shi. An kuma gan shi tare da mutanensa a fadarsa a daren Laraba.

Maude yana daya daga cikin tsofaffin sarakunan gargajiya a jihar Kaduna.

El-Rufai ya sanar da kokarin da ake na ceto Sarkin Jaba

Gwamnatin jihar Kaduna tace tana aiki tare da gwamnatin jihar Nasarawa da kuma jami'an tsaro daga jihohin biyu wurin ceto sarkin Jaba, Gyet Muade wanda miyagun 'yan bindiga suka sace a ranar Litinin, Channels TV ta wallafa.

Miyagun 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace basaraken mai shekaru tamanin da uku a duniya yayin da yake gonarsa dake yankin Gitata na jihar Nasarawa wanda ke da iyaka da Jaba a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba

Kamar yadda ChannelsTV ta ruwaito, a yayin jawabi ga wasu jami'an gwamnati da hukumomin tsaro a fadarsa dake masarautar Jaba, Gwamna El-Rufai ya samu wakilcin kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel