‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar dokokin Jigawa, Haladu Bako

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar dokokin Jigawa, Haladu Bako

  • An sace tsohon dan majalisar dokokin jihar Jigawa, Haladu Bako Uza wanda ya wakilci mazabar Auyo a majalisar dokokin jihar
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne suka sace tsohon dan majalisar a kan hanyar Kano zuwa Hadejia a daren ranar Laraba
  • Kakakin 'yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin

Jihar Jigawa - ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Jigawa, Haladu Bako.

An yi garkuwa da Mista Bako ne a daren ranar Laraba yayin da yake tafiya daga Kano zuwa jihar Jigawa, Mansur Ahmed, mai taimaka wa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido kan harkokin yada labarai ya bayyana, jaridar Premium Times ta ruwaito.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar dokokin Jigawa, Haladu Bako
Masu garkuwa da mutane sun sace tsohon dan majalisar dokokin Jigawa Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Mista Ahmed ya bayyana cewa Mista Bako ya wakilci karamar hukumar Auyo a majalisar jihar daga 2007 zuwa 2015.

Mista Bako, jigo a jam'iyyar People Democratic Party (PDP) a Jigawa, ya kuma tsaya takarar amma kuma ya sake rasa kujerar a shekarar 2019.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa ASP Lawan Shiisu Adam, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da 'yan bindigar, wadanda yawansu ya kai biyar, suka tare Ringim zuwa garin Gujungu tare da yi wa masu motoci fashi.

ASP Lawan ya bayyana cewa 'yan fashin sun harbe wani direban mota a yayin harin.

Ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin, jami'an 'yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru kuma sun gano harsasai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa, an hada tawagar sintiri domin ceto wanda lamarin ya rutsa da shi.

A wani labari na daban, dan takarar jam'iyyar All Progressive Chairmanship Congress (APC) na karamar hukumar Kachia na jihar Kaduna, Alamkah Dominic Usman wanda aka fi sani Cashman ya sheka lahira bayan wasu miyagun 'yan bindiga sun harbe shi a jihar Benue.

A yayin zantawa da Daily Trust, shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Kachia, Alhaji Ahmed Tijjani Sulaiman, ya ce an harbe Usman a wani wuri a jihar Benue.

Alhaji Sulaiman ya ce, Usman amintaccen dan jam'iyya ne kuma ya hadu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Binuwai inda iyalinsa ke zama, bai san cewa yana dab da amsa kiran ubangijinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel