Sunday Igboho ya ji mummunan rauni lokacin da DSS suka kai hari gidansa, Lauyansa
- Lauyan Igboho ya ce mutumin ya jigata sosai kuma yana bukatan ganin Likita
- Ya mika bukata ga kotu a bashi beli don ya kula da kansa
- Igboho ya tsallake rijiya da baya yayinda DSS suka kai harin gidansa a farkon watan yuli
Mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho, ya samu munanan raunuka lokacin da jami'an hukumar DSS suka kai masa hari gidansa dake Soka, Ibadan, jihar Oyo.
A ranar Alhamis, 1 ga Yuli, 2021, hukumar DSS ta kai samame gidan Igboho.
Lauyansa na kasar Benin, Ibrahim Salami, ya bayyana hakan a hirar da yayi ranar Talata, rahoton ThePunch.
Ya yi bayanin cewa har yanzu Igboho na jinyan raunuka.
A cewarsa, Sunday Igboho na bukatan a bashi beli saboda ya kula da kansa.
"Ina kira ga iyalansa da magoya bayansa suyi hakuri kuma su cika da addu'a. Lokacin da suka kai hari gidansa a Najeriya, ya yi tsalle ne daga saman gini kuma kirjinsa ya samu rauni. Ya jigata sosai."
"Kai ko tsayuwa ya gaza yi gaban Alkali. A zaune yayiwa Alkali magana. Yana bukatan a sakeshi saboda ya kula da kansa."
Harin da DSS ta kai gidansa
A harin da DSS ta kai, an damke abokansa 13 kuma an hallaka 2.
Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bayyana hakan a hirar da yayi da manema labarai cewa sun samu labarin Sunday Igboho na boye makamai a gidansa.
Sunday Igboho ya gurfana a kotu a Kwatano don sanin makomarsa
A ranar Litinin ne Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa ya bayyana a Kotun daukaka kara a Kwatano inda yake gab da fuskantar shari'a, The Nation ta ruwaito.
Bayan kimanin awanni shida ana zama, kotu ta bada umurni a mayar da shi gidan yari.
Asali: Legit.ng