An damke kasurgumin dan bindiga da aka dade ana nema a jihar Sokoto

An damke kasurgumin dan bindiga da aka dade ana nema a jihar Sokoto

  • Dubun wani shahrarren dan bindiga ya cika a jihar Sokoto
  • Jami'an NSCDC sun damke ranar Talata yayinda ya shiga gari siyayya
  • Sun ce magungunan kara karfin maza yayin jima'i ya je saye

Sokoto - Wani kasurgumin dan bindiga wanda aka dade ana nema a jihar Sokoto ya shiga hannun jami'an hukumar tsaron kare farin kaya watau NSCDC.

Kwamadandan hukumar NSCDC a jihar Sokoto, Saleh Dada, ya bayyanawa manema labarai yadda aka kamashi ranar Laraba, rahoton TheCable.

Kwamandan yace an dade ana neman Galadima ruwa a jallo.

Dada ya kara da cewa an damkeshi ne ranar Talata a mabuyarsa dake Aliyu Jodi a cikin Sokoto.

Kwamandan yace Galadima ya shiga hannu ne yayinda ya fito gari neman maganin karfin maza ga mabiyansa.

Ya yi bayanin cewa an samu labarin leken asiri kansa ne saboda yadda suka addabi alummar Hamma Ali.

Jami'an sun jinjinawa mutan garin da suka ba da labari kan yan bindigan kuma sun tabbatar musu da cewa za'a basu isasshen tsaro.

Kara karanta wannan

Hoton Hatsabibin Ɗan Bindigan Sokoto Da Aka Kama a Gidan Karuwai Bayan Shafe Shekaru Ana Nemansa Ruwa a Jallo

An damke kasurgumin dan bindiga da aka dade ana nema a Sokoto
An damke kasurgumin dan bindiga da aka dade ana nema a jihar Sokoto Hoto: NSCDC
Asali: Facebook

Babbar Magana: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibai Da Dama a Makarantar Sojoji

A bangare guda, yan bindiga sun yi awon gaba da Dalibai dama a jihar Edo na kwalejin sojojin ruwa dake Sepele, Jihar Delta, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne ranar Litinin yayin da ɗaliban suke kan hanyarsu ta komawa Sepele daga jihar Kaduna.

Maharan sun farmaki motar Bas mai ɗaukar mutum 18 dake ɗauke da ɗaliban, inda suka tasa su zuwa wani wuri da ba'a sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel