A gaskiya Gwamna Ganduje ya na mana shisshigi a shari’ar Abduljabbar Kabara inji Lauyoyinsa

A gaskiya Gwamna Ganduje ya na mana shisshigi a shari’ar Abduljabbar Kabara inji Lauyoyinsa

Lauyoyin Abduljabbar Nasir Kabara sun ce gwamnati na yi wa shari’a katsalandan

Barista Saleh M. Bakaro ya ce bai kamata Gwamnan Kano ya fito, ya na magana ba

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi wasu kalamai yayin da shari’ar ta ke kotu

Lauyoyin da suka tsaya wa babban malamin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, suna zargin gwamnati da tsoma kanta a cikin shari’ar da ake yi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto lauyoyin shehin suna cewa Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya na shisshigi a shari’ar da ake yi da malamin.

Lauyoyin sun yi kira ga masu ruwa da tsaki a wannan kara da ke kotu, da su sa wa gwamnatin Kano idanu sosai domin tabbatar da cewa gaskiya ta yi aiki.

Rahoton ya ce lauyoyin sun yi wannan jawabi ne yayin da su ka kira wani taron manema labarai a garin Kano, a yammacin Lahadi, 25 ga watan Yuli, 2021.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

Barista Saleh M. Bakaro ne ya jagoranci sauran lauyoyin, inda su ka yi wannan kira a dazu da yamma, lauyan ya ce ana kokarin bata wa shehin suna.

Saleh M. Bakaro ya ke cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fito ya na yin maganganun da za su iya jawo matsala a wannan shari’ar da ke gaban Alkali.

Gwamna Ganduje da Abduljabbar Kabara
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Asali: UGC

“Abin da ya jawo za mu gabatar maku da jawabi a yau shi ne abin takaicin da ke faru wa, inda mai girma gwamnan Kano yake wasu kalamai masu tada hankali.”
“Mu na ganin wadannan kalamai da ke fito wa kafin a karkare shari’a, barazana ne ga neman adalcin da wanda mu ke kare wa, Abduljabbar Nasiru Kabara, ya ke yi.”
“Gwamna ya ce shi ya kawo dokar da ta sa aka tsare wanda mu ke kare wa a gidan yarin Kano”
“Ya karkare cewa Kabara ya zagi janibin Manzon Allah (SAW), ko da cewa maganar ta na gaban kotu domin ayi shari’a, kuma Kabara bai amsa laifinsa ba.”

Kara karanta wannan

Ba don Buhari ba da ‘yan Najeriya sun shiga halin wayyo Allah – Sarkin Daura

A baya an ji cewa Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi furuci kan lamarin Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara wanda aka kai kararsa.

Abdullahi Umar Ganduje ya yi jawabi ne a lokacin da ya kai ziyarar gaisuwar sallah a gidan shugaban darikar kadriyya watau Sheikh Qaribullahi Kabara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel