Bayan kwanaki 67 a garkame, 'yan fashi sun sako mutane 4 da suka yi garkuwa da su a matsayin goron Sallah

Bayan kwanaki 67 a garkame, 'yan fashi sun sako mutane 4 da suka yi garkuwa da su a matsayin goron Sallah

  • Akalla mutane 6 da barayi suka sace daga garin Batsari da ke cikin jihar Katsina sun sake haduwa da danginsu
  • Rahotanni sun bayyana game da yadda 'yan bindigar suka saki wadanda suka sace a matsayin goron Sallah ga kauyensu
  • Sai dai kuma, sauran mazauna yankin da aka sace tare da wadanda aka sako suna garkame a hannun masu garkuwa da mutanen

Shida daga cikin mutane 28 da 'yan fashi suka sace daga garin Batsari na jihar Katsina sun samu ‘yanci.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an sace mutanen ne a watan Mayu tare da wasu mutane 22 lokacin da ‘yan bindigan suka kai mamaya garin.

Bayan kwanaki 67 a garkame, 'yan fashi sun sako mutane 4 da suka yi garkuwa da su a matsayin goron Sallah
'Yan bindiga sun saki wasu mutane a matsayin goron Sallah a jihar Katsina Hoto: @MasariMediaCenter
Asali: Facebook

Legit.ng, ta tattaro cewa yan sanda da hukumomin gwamnati basu tabbatar da ci gaban ba.

Bayan sun kame mutanen na tsawon kwanaki 67, 'yan bindigar sun bayyana cewa an saki 4 daga cikin mutanen 6 ne a matsayin goron Sallah ga al’umman garinsu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

Kafar labaran ta ruwaito cewa wasu majiyoyin yankin sun bayyana cewa yan fashin a yammacin ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli, sun ce za a saki wata mata da danta a lokacin da mijinta, Umar Tukur, ya biya kudin fansa naira miliyan 2.5.

Wani mazaunin garin mai suna Misbahu Batsari ya ce lokacin da masu laifin za su saki wadanda aka sacen, sun yanke shawarar zabar wasu mutane hudu a matsayin goron Sallah ga mutanen yankin.

Batsari ya ci gaba da bayanin cewa an dauki wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda suka fito daga gida daya zuwa asibiti domin duba lafiyarsu.

Sai dai, ya ce al'umman ba su da masaniya kan dalilin da ya sa 'yan fashin suka aikata hakan.

A wani labarin, wadansu ‘yan fashi da makami a safiyar ranar Juma’a sun kai hari kan makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Unguwar Sarki, a cikin garin Kaduna inda suka tafi da takardun jarrabawa da aka shirya wa daliban aji shida wadanda za su rubuta jarrabawar karshe ta NECO bisa tsammanin cewa kudade ne.

Kara karanta wannan

Hoton Matar Da Ta Haɗa Baki Da Mijinta Don Ƙaryar Garkuwa Da Ita a Jihar Niger

‘Yan bindigar da suka kutsa kai cikin makarantar sun nemi jami’ar da ke mai kula da NECOn da ta mika musu takardun jarrabawar duk da cewa ta yi kokarin bayyana musu takardun jarrabawar ne ba kudade ba.

An gano cewa sun kwace takardun jarrabawar da ke nannade a cikin kunshi tare da takardun amsa jarrabawar inda suka tafi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng