Da dumi-dumi: Buhari ya jagoranci muhimmin taro a Landan

Da dumi-dumi: Buhari ya jagoranci muhimmin taro a Landan

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taro mai muhimmanci a birnin Landan
  • Taron na zuwa ne gabanin gabatar da jawabinsa a taron ilimi na duniya kan hadin kai wajen zuba kudi fagen ilimi (GPE) 2021-2025
  • Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai hadiminsa, Femi Adesina, ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama tare da sauran jami’an gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron dabaru gabanin gabatar da jawabinsa a taron ilimi na duniya kan hadin kai wajen zuba kudi fagen ilimi (GPE) 2021-2025 a Landan.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafin Facebook a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli.

Da dumi-dumi: Buhari ya jagoranci muhimmin taro a Landan
Buhari ya jagoranci wani taro mai muhimmanci a birnin Landan Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Kodayake ba a sami cikakken bayani kan ajandar taron ba, ana sa ran zai kasance game da taron wanda ke da nufin aiki don taimakawa wajen sauya tsarin ilimi a kasashe da yankuna da dama.

Kara karanta wannan

PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya

Adesina, ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama tare da sauran jami’an gwamnati sun kasance a cikin taron.

Zai kuma gana da Firayim Ministan Biritaniya Boris Johnson.

Idan za ku tuna, Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Landan, kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa da kuma halartan taron kasa da kasa kan inganta ilimi a duniya.

Buhari ya isa Ingila da cikin dare a jirgin shugaban kasa Eagle001.

Ya samu kyakkyawan tarba daga Jakadan Najeriya dake Landan, Amb. Sarafa Ishola, da shugabar yankin Sussex, Mrs Jennifer Tolhurst, da kuma Mr David Pearey.

PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya

A gefe guda, Jam'iyyar PDP ta soki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan domin duba lafiya da kuma halartar wani taron koli kan fannin ilimi duk dai a Landan din, jaridar Punch ta ruwaito.

PDP ta ce, tafiyar shugaban ba komai bane face son amfani da albarkatun kasa don halartar taro wanda zai iya halartar ta yanar gizo; kamar yadda wadanda suka shirya taron suka tsara.

Kara karanta wannan

2023: Ku Tashi Ku 'Ƙwace' Mulki Daga Hannun Dattijai, Gwamna Ya Zaburar Da Matasan Nigeria

PDP ta kuma yi Allah wadai da Fadar Shugaban Kasa kan kokarin boye ganawarsa ta sirri da likitocinsa a karkashin taron da zai halarta, tare da yin tir da rashin cika alkawuran shugaba Buhari na zaben 2015 cewa ba zai je kasar waje domin duba likita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel