Bayan hallaka DPO, 'Yan sanda sun sake cafke wani bokan kungiyar ta'addanci ta IPOB
- Rundunar 'yan sanda a jihar Imo sun samu nasarar kame bokan 'yan kungiyar ta'addanci ta IPOB
- Tuni aka zarce dashi hedkwatar 'yan sanda inda ya yi bayanai masu amfani wajen kame sauran masu laifi
- Wannan na zuwa ne jim kadan bayan hallaka wani DPO na 'yan sanda a wani yankin jihar ta Imo
Jihar Imo - Tawagar wasu 'yan sanda na rundunar 'yan sanda ta jihar Imo ta cafke bokan da ke shirya layu ga mambobin kungiyar IPOB da ESN a cikin Jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.
Wanda ake zargin, Benneth Okoli, mai shekaru 49, an kama shi ne a hubbarensa da ke Akuma a karamar hukumar Oru ta Gabas ta Jihar ta Imo.
A yau Alhamis 29 ga watan Yuli ne aka gurfanar da wanda ake zargin a hedikwatar rundunar 'yan sanda da ke Owerri bayan gudanar da binciken kwakwaf da tattara bayanan sirri na cewa yana shirya layu ga 'yan bindiga a hubbarensa, in ji kwamishinan 'yan sandan jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa, 'yan bindigan sukan karbi layar maganin bindiga da harsasai da wukake a wurin bokan kafin su far wa ofisoshin 'yan sanda a yankin.
A cewarsa:
“Nan da nan aka killace hubbaren sannan tawagar 'yan sandan suka shiga cikin dabara, inda aka kama bokan, Benneth.
Lokacin da ake bincike a wurin, ya ce an gano daya abubuwan fashewa hadin gida, layu daban-daban, da kuma ciyar da ake zargin tabar wiwi ce a cikin jaka.
A cewarsa, wanda ake zargin, a lokacin da aka yi masa tambayoyi, ya gabatar da bayanai masu amfani wanda a halin yanzu ke taimaka wa ‘yan sanda wajen cafke ragowar tawagarsa da suka gudu a halin yanzu.
Yayinda yake Allah wadai da ta'addancin 'yan ta'addan musamman harin da aka kaiwa Omuna inda wani DPO ya rasa ranta, shugaban 'yan sanda, ya yaba da jarumtar da jami'an da rundunar suka nuna tare da neman su ci gaba da aiki tukuru.
Sojoji sun garkame kasuwannin jihar kudu saboda nuna goyo baya ga Nnamdi Kanu
Sojoji a ranar Talata sun hana ‘yan kasuwa a kasuwannin katako da na kayayyakin gini a Orlu, jihar Imo, budewa domin gudanar da kasuwancinsu na ranar.
Mafi yawan ‘yan kasuwar a kasuwannin biyu a ranar Litinin din da ta gabata sun ki bude shagunansu don nuna goyon baya ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar tuhumar ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Sojojin, wadanda ke gudanar da aikin shingen binciken ababen hawa kusa da manyan kasuwannin biyu a Orlu, sun hana ‘yan kasuwar bude shagunansu da duk wata harkar kasuwanci.
'Yan kasuwar sun shaida wa wakilin jaridar Punch cewa sojoji sun umarci masu gadin kasuwarda kada su bude kofofin kasuwannin.
Rikicin Kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar ta-baci a wasu yankuna 7
A wani labarin na daban, A ranar Talata ne Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kan wasu al’ummu bakwai da ke karamar hukumar Balanga ta jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ismaila Uba-Misilli, Darakta-Janar na harkokin yada labarai, na gidan gwamnatin Gombe ya fitar.
Mista Uba-Misilli ya ce Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Njodi ne ya bayyana hakan. An ruwaito Mista Njodi yana cewa matakin ya biyo bayan sake barkewar rikici tsakanin kabilun Lunguda da Waja a cikin al'ummomin a safiyar Talata 27 ga watan Yuli, VON ta ruwaito.
Asali: Legit.ng