Gwarazan Yan Sanda Sun Cafke Wani Tsageran IPOB Dauke da Muggan Makamai
- Gwarazan yan sanda a jihar Imo, sun samu nasarar kama wani tsageran kungiyar IPOB dauke da makamai
- Rundunar yan sandan jihar ta bayyana cewa jami'anta sun samu wannan nasara ne da haɗin guiwar NDLEA
- Rundunar tace ana cigaba da bincike domin zakulo ragowar yan ta'addan bayan samun bayanan suna yawo a cikin gari
Imo:- Rundunar yan sanda ta jihar Imo, tace ta cafke wani da ake zargin mamban kungiyar ESN-IPOB ne ɗauke da makamai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, shine ya bayyana haka, yace an kwato sinkin alburusai a hannunshi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Abattam yace wanda ake zargin yana daga cikin mutanen dake aikata ta'addanci a kan mutanen yankin Umueli Amaraku, kamar hukumar Mbano, jihar Imo.
Yace: "Bayan mun samu bayanin cewa wasu ragowar yan ta'addan ESN-IPOB na yawo a yankin, bayan an tarwatsa sansanin su."
"Kwamishinan yan sanda, Abutu Yaro, ya umarci 'Rundunar bincike da bankado masu laifi' nan take su fara gudanar da bincike."
"Yayin wannan binciken ne jami'an suka kama wani Obumneke, a kan hanyarsa. Bayan bincikarsa mutumin ya amsa cewa shi ɗan IPOB ne."
Wane makamai aka kwato daga hannunsa?
Abattam ya ƙara da cewa jami'an yan sanda sun gudanar da binciken ne tare da haɗin guiwar jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA.
Daga cikin makaman da aka kwato a hannun wanda ake zargin akwai ƙaramar bindigar hannu kirar ƙasa cike da harsashi, da kuma wasu harsasan da aka yi amfani da su.
Kakakin yan sandan ya kara da cewa a halin yanzun ana cigaba da gudanar da binciken domin zaƙulo ragowar yan ta'addan.
A wani labarain kuma Babbar Magana: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibai Da Dama a Makarantar Sojoji
Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da ɗaliban kwalejin sojojin ruwa dake Sepele, jihar Delta.
Rahoto ya nuna cewa maharan sun kai wa motar bus ɗin ɗaliban hari har suka tafi da su.
Asali: Legit.ng