Sunaye: An ambaci Jonathan da wasu yayin da majalisa ta gano AGF ya cire N665.8bn ba bisa ka’ida ba

Sunaye: An ambaci Jonathan da wasu yayin da majalisa ta gano AGF ya cire N665.8bn ba bisa ka’ida ba

  • Majalisar Dattawa ta ce an cire biliyan N665.8 daga Asusun Bunkasa Albarkatun Kasa da Kudaden Zaman Lafiya ba bisa ka’ida ba tsakanin 2004 da 2015
  • A cewar majalisar, kudaden wanda yake mallakar matakai uku na gwamnatin an tanade su ne domin bunkasa wasu albarkatun karkashin kasa banda mai da iskar gas
  • Sai dai kuma, ofishin AGF ya cire biliyan N665.8 don wasu dalilai, gami da biyan hakkin tsohon Shugaba Jonathan

Harabar majalisar kasa, Abuja - Majalisar Dattawa ta zargi Ofishin Akanta Janar na Tarayyar da cire biliyan N665.8 ba bisa ka’ida ba daga Asusun Bunkasa Albarkatun Kasa da Kudaden Zaman Lafiya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ’yan majalisar sun kara da cewa an cire kudaden a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2015 kuma aka ba da su a matsayin rance ga hukumomin gwamnati daban-daban, sabanin manufar kafa asusun.

Sunaye: An ambaci Jonathan yayin da majalisa ta gano AGF ya cire N665.8bn ba bisa ka’ida ba
Ofishin Akanta-Janar ya ciri N665.8bn ba bisa ka’ida ba Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa zargin na kunshe ne a cikin rahoton kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati.

Kara karanta wannan

Ba zamu sayarwa Najeriya makamai ba saboda zaluncin da jami'anta keyi: Yan Majalisar Amurka

Kwamitin ya kasance yana binciken kudaden da hukumomin gwamnatin tarayya suka kashe daga 2015-2018 bisa la’akari da rahoton binciken kudi daga babban Odita-Janar na Tarayyar.

Kwamitin ya gabatar da rahoton bincikensa na watanni shida a kan Asusun Tarayya na shekara ta 2015 wanda majalisar dattawa ta amince da shi kafin tafiya hutun shekara.

Majalisar Dattawan ta bayyana cewa manufar Asusun Bunkasa Albarkatun Kasa shi ne samar da kudade don bunkasa wasu albarkatun karkashin kasa banda mai da iskar gas.

Ta kara da cewa asusun zai samar da tallafi idan aka samu koma bayan tattalin arziki; kuma masu cin gajiyar su ne jihohi 36 da Birnin Tarayya kuma asusun karfafa gwiwa na matakai uku ne na gwamnati.

Sai dai kuma, an kashe kudade don wasu dalilai, jaridar ThisDay ya ruwaito.

A ƙasa akwai jerin 'yan siyasa da hukumomin gwamnati da rahotanni suka ce sun ci gajiyar kudaden da ake zargi an karkatar:

Kara karanta wannan

Majalisar a Zamfara ta nemi matamakin gwamna ya bayyana a gabanta cikin sa'o'i 48

1. Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

2. Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo (an biya tsoffin shugabannin biliyan N1.5 haƙƙoƙin daga asusun a 2015)

3. INEC (Naira biliyan 20)

4. Ruduar Sojojin Najeriya

5. Hukumar Kula da Tashar Jiragen Sama na Tarayya (FAAN) da wasu Ma’aikatu, Sassa da Hukumomi (MDAs)

Majalisar Dattawa, a cikin kudurin ta, ta umarci Ofishin Akanta-Janar na Tarayya da ya tabbatar da mayar da kudaden cikin kwana 60.

Jerin sunaye: Gwamnan CBN, Shugaban NNPC da sauran manyan gwamnati da kwamitin majalisa ke so a kama

A wai labarin, kwamitin majalisar wakilai kan asusun gwamnati ya ba da shawarar a bayar da izinin kama wasu fitattun shugabannin hukumomin gwamnati.

A cewar jaridar The Punch, kwamitin ya bayar da wannan shawarar ne a cikin rahoton binciken da ya fito daga ofishin mai bincikar kuɗi na ƙasa na shekarun 2014 zuwa 2018.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Gwamnan CBN, Shugaban NNPC da sauran manyan gwamnati da kwamitin majalisa ke so a kama

Legit.ng ta tattaro cewa har yanzu rahoton kwamitin dai yana jiran majalisar tayi nazari a kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel