Ba zamu sayarwa Najeriya makamai ba saboda zaluncin da jami'anta keyi: Yan Majalisar Amurka
- Amurka ta fasa sayarwa Najeriya makaman biliyoyin Naira
- Wannan ya biyo bayan isowar jiragen Super Tucano 6 cikin 12 da akayi oda
- Gwamnatin Donald Trump ce ta sayarwa Najeriya a baya amma ta Joe Biden tace ba zai yiwu ba
Yan majalisar dokokin Amurka sun hana sayarwa Najeriya jiragen yaki masu saukar angulu bisa zalunci da take hakkin bil-adama da gwamnatin Buhari tayi.
Cinikayyar da aka yi na kudi $875million don sayan jiragen Cobra attack helicopter guda 12 ya fuskanci kalubale ne yayinda zaman kwamitin majalisar dattawa na harkokin wajen Amurka.
Bayan Jiragen yakin, Najeriya ta nemi a sayar mata da injinonin jirage masu saukar Angulu 28 da GE Aviation ya kera, na'urorin bibiyan jiragen yaki 14 da kamfanin Honeywell ya kera, da rokokin zamani 2,000.
Jawabin da aka saki a shafin kwamitin na yanar gizo ya nuna cewa ma'aikatar wajen Amurka ce ta fara aikewa majalisa rahoton cinikin a Junairu kafin nada Joe Biden matsayin shugaban kasar Amurka.
Rahoton ya nuna cewa yan majalisar Amurka sun shiga tsaka mai wuya tsakanin taimakawa Najeriya wajen magance matsalar tsaro da kuma take hakkin bil-adaman da takeyi.
Yan majalisar sun nuna bacin ransu kan yadda gwamnatin Buhari ke take hakkin bil-adama da cin zarafin da jami'anta keyi.
Shin menene hujjar yan Majalisar?
Daga cikin misalan da suka ambata akwai dakatar da Shafin Tuwita, kisan matasa yayin zanga-zangar #EndSARS a bara, dss.
Shugaban kwamitin, Bob Menendez, ya yi kira ga "sake nazari kan alakar kasar Amurka da Najeriya" yayin zaman da majalisar tayi da Sakataren wajen Amurka, Anthony Blinken, a Yuni.
Bugu da kari, rahoton shafin ya ce manyan Sanatocin majalisar sun ce a dakatar da sayar da makaman.
Rahoton ya ruwaito wani dan Najeriya mai bahasi a hukumar kare hakkin bil-adama, Human Rights Watch, Aniete Ewang, da cewa:
"Akwai dabi'ar cin zarafi da jami'an Sojojin Najeriya ke yi. Akwai rikice-rikice a kasar yanzu. Kuma ina ganin gwamnati na kokarin kare rayukan mutane da dukiyoyinsa amma wajibi ne ayi hakan bisa ka'idojin kare hakin mutane."
"Ba zai yiwu ayi watsi da daya domin cimma dayan ba."
Jiragen Yaƙin Tucano 6 Da Najeriya Ta Saya Daga Amurka Sun Iso Nigeria
Rundunar sojojin saman Nigeria, NAF, a ranar Alhamis ta karbi rukuni na farko na jiragen sama na yaki kirar A-29 Super Tucano daga kasar Amurka.
Edward Gabkwet, direktan sashin hulda da jama'a da watsa labarai na hedkwatar rundunar sojojin saman Nigeria da ke Abuja ne ya sanar da hakan.
Bashir Magashi, Ministan tsaro; Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin kasa; da Oladayo Amao, babban hafsan sojojin sama ne suka karbi jiragen a Kano.
Asali: Legit.ng