Tauraruwar Kannywood Maryam Yahaya Ta Bayyana Cutar Dake Damunta Yasa Aka Ji Ta Shiru

Tauraruwar Kannywood Maryam Yahaya Ta Bayyana Cutar Dake Damunta Yasa Aka Ji Ta Shiru

  • Matashiyar jarumar Kannywood, Maryam Yahaya, ta bayyana wasu cututtuka biyu dake damunta
  • Maryam ta yi watsi da jita-jitar cewa an mata asiri, inda ta bayyana cewa zazzabin maleriya da taifod ne ke damunta
  • Mahaifinta, Yahaya Yusuf, yace ɗiyarsa ta kwana biyu a kwance kuma har asibiti suka kaita

Kano:- Ɗaya daga cikin fitattun jarumai mata dake tashe a masana'antar shirya fina-fanai Kannywood, Maryam Yahaya, tace cutar taifod da Maleriya ke damunta.

Jarumar ta faɗi hakane yayin wata fira da tayi da BBC Hausa, tace wannan dalilin ne yasa aka daina ganinta a cikin sabbin fina-finan Hausa.

Maryam Yahaya ta kuma yi watsi da wata jita-jita da mutane ke yaɗawa a kanta cewa tana fama da cutar iska wato jifan aljanu.

Tauraruwar Kannywood Maryam Yahaya
Tauraruwar Kannywood Maryam Yahaya Ta Bayyana Cutar Dake Damunta Yasa Aka Ji Ta Shiru Hoto: @real_maryamyahaya
Asali: Instagram

Wakilin BBC da ya ziyarci jarumar har gidansu, ya bayyana cewa ta yi matuƙar ramewa.

Maryam Tace: "Na yi taifod da maleriya ne, ina kan yi. Amma yanzu jiki Alhamdulillahi, na samu lafiya."

Kara karanta wannan

Na'uarar CCTV ta nuna yadda yar shekara 9 ta haddasa gobarar katafaren kantin Prince Ebeano a Abuja

Dagaske ne an mata asiri ko jifar Aljanu?

Da aka tambayeta kan jita-jitar da wasu ke yaɗawa cewa an mata asiri ko an jefe ta da aljanu, Maryam tace: "Maganar gaskiya ni ba jifa ba ne ya dame ni don ban ma san shi ba."

A cewar matashiyar tauraruwar ta kwashe fiye da wata ɗaya tana jinyar rashin lafiya amma yanzun ta samu sauki sosai "sai dai rashin ƙwari kuma dama sai a hankali ƙwari yake zuwa."

Mahaifin Maryam, Yahaya Yusuf: Ko dagaske ne an jefi ɗiyarka?

Ana shi ɓangaren mahaifin maryam, Alhaji Yahaya Yusuf, ya bayyana cewa ɗiyarsa ta kwan biyu tana fama da cutar taifod da Maleriya.

Alhaji Yahaya ya yi wasti da raɗe-raɗin cewa an yiwa ɗiyarsa asiri ko an jefe ta da aljanu.

Yace zazzabi ne ke damunta kuma an kaita Asibiti sannan ana haɗawa da maganin gargajiya.

Matashiyar mai shekara 20, Maryam Yahaya, ta fara jan zaren ta ne a fim ɗinta na fatko wato Mansoor wanda Ali Nuhu ya bada umarni.

Kara karanta wannan

Ina bukatar miji, Budurwa mai son daidaituwar 'yancin mata da maza ta koka

A wani labarin kuma Yan Bindigan da Suka Sace Basaraken Gargajiya Mai Daraja Ta Daya a Kaduna Sun Kira Iyalansa Ta Wayar Salula

Yan bindigan da suka sace basarake mai muhimmanci a masarautar Jaba, Kpop Ham, Gyet Maude, sun tuntubi makusantansa.

Ɓarayin sun kira iyalansa ta wayar salula, inda suka nemi a biya su kuɗin fansa har naira miliyan N100m, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel