Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu

  • Cikin dare, shugaban kasan Najeriya ya isa Ingila
  • Buhari zai kwashe kimanin makonni biyu a kasar Sarauniya Elizabeth
  • Buhari ya tafi domin duba lafiyarsa da kuma halartan taro

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Landan, kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa da kuma halartan taron kasa da kasa kan inganta ilimi a duniya.

Buhari ya isa Ingila da cikin dare a jirgin shugaban kasa Eagle001.

Ya samu kyakkyawan tarba daga Jakadan Najeriya dake Landan, Amb. Sarafa Ishola, da shugabar yankin Sussex, Mrs Jennifer Tolhurst, da kuma Mr David Pearey.

Fadar shugaban kasa ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki da safiyar Talata, 27 ga Yuli, 2021.

Kalli hotunan saukarsa:

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari ya tafi Ingila

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, 26 ga Yuli, zai shilla kasar Birtaniya ganin Likitocinsa da kuma halartan taron ilimi na duniya kan hadin kai wajen zuba kudi fagen ilimi watau GPE 2021-2025.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sunday Igboho ya isa kotu a Kwatano don sanin makomarsa

Bayan haka shugaba Buhari zai yi zaman diflomasiyya da Firai Minista Boris Johnson.

Adesina yace:

"Bayan taron, shugaban kasa zai kwashe yan kwanaki domin ganin Likitansa da ya kamata ace ya gani tun a baya. Zai dawo Najeriya a tsakiyar Agusta, 2021."

Adesina ya kara da cewa Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; karamin ministan Ilimi, Emeka Nwajuiba; NSA Babagana Munguno, da shugaba NIA, Ahmed Rufai Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel