Jerin Sunayen Kasashe 13 da Saudiyya Ta Hana Gudanar da Aikin Umrah Saboda Wannan Dalilin

Jerin Sunayen Kasashe 13 da Saudiyya Ta Hana Gudanar da Aikin Umrah Saboda Wannan Dalilin

  • Hukumomi a kasar Saudiyya sun hana wasu kasashen duniya 13 zuwa aikin umrah
  • Saudiyya tace an ɗauki wannan matakin ne saboda yadda cutar COVID19 ke cigaba da yaɗuwa a kasashen
  • Hakanan Saudiyya tace duk wanda yaje waɗannan kasashen to ya killace kanshi na mako 2

Hukumar dake kula da masallatai biyu masu tsarki a kasar Saudiyya ta bayyana sunayen wasu kasashe 13 da ba'a amince su je aikin umrah da aka buɗe kwanan nan ba.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da shafin Haramain Sharifain na dandalin sada zumunta facebook ya fitar ranar Laraba.

A jikin takardar, Saudiyya ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne saboda karuwar masu harbuwa da cutar COVID19 a kasashen.

Saudiyya ta hana kasashe 13 aikin Umrah
Jerin Sunayen Kasashe 13 da Saudiyya Ta Hana Gudanar da Aikin Umrah Saboda Wannan Dalilin Hoto: Haramain Sharifain FB Fage
Asali: Facebook

Hakanan kuma Saudiyya tace ba wai aikin Umrah kaɗai aka hana mutanen waɗannan ƙasashen ba harda shiga ƙasa baki ɗaya.

Wane kasashe ne hanin ya shafa?

Kasashen da wannan hanin ya shafa sun haɗa da Afghanistan, Argentina, Brazil, Masar da Habasha

Kara karanta wannan

2023: Ku Tashi Ku 'Ƙwace' Mulki Daga Hannun Dattijai, Gwamna Ya Zaburar Da Matasan Nigeria

Sauran sune, Indiya, Indonesia, Lebanon, Pakistan, Afirka Ta Kudu, Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wani ɓangaren takardar, tace: "Duk mutanen da suke son shiga Saudiyya da suka je wadannan kasashen, sai sun killace kansu na makwanni 2, kafin su fara batun zuwa kasa mai tsarki."

"Ma'aikatar cikin gida na cigbaa da bibiyar kasashen duniya kan yaɗuwar cutar korona, kuma za'a iya ƙara wasu kasashen nan gaba ba tare da sanarwa ba."

Saudiyya ta shawarci musulmin duniya da su ziyarci ofishin jakadamcinta dake kasashen su domin sanin ko kasar su na cikin hanin kafin su ɗaura ɗamarar tafiya.

A wani labarin kuma Babbar Magana: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibai Da Dama a Makarantar Sojoji

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da ɗaliban kwalejin sojojin ruwa dake Sepele, jihar Delta.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun kai wa motar bus ɗin ɗaliban hari har suka tafi da su.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Miliyan 85m Zasu Rasa Aikinsu, Inji Ministan Buhari Ya Fadi Dalili

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262