Yan Najeriya Miliyan 85m Zasu Rasa Aikinsu, Inji Ministan Buhari Ya Fadi Dalili

Yan Najeriya Miliyan 85m Zasu Rasa Aikinsu, Inji Ministan Buhari Ya Fadi Dalili

  • Ministan Shugaba Buhari ya bayyana cewa kimanin yan Najeriya miliyan 85m ka iya rasa aikinsu
  • Karamin ministan kimiyya da fasaha, Mohammed Abdullahi, yace hakan zai faru ne saboda rashin ilimin fasahar zamani
  • Gwamna Ganduje ya bayyana yadda gwamnatinsa ta ɗauki matakin baiwa matasa horo domin dogaro da kansu

Ƙaramin ministan kimiyya da fasaha, Mr. Mohammed Abdullahi, ya bayyana cewa kimanin yan Najeriya miliyan 85m suna kan siraɗin rasa ayyukansu saboda rashin ilimin fasahar zamani da kwarewa, kamar yadda thisday ta ruwaito.

Ministan ya faɗi haka ne a wurin taron kaddamar da shirin samarwa matasa yan Najeriya miliyan 20m ayyukan yi daganan zuwa shekarar 2030.

Abdullahi yace ma'aikatarsu tana amfani da tsarin da take da shi yanzun tare da kudirin baiwa matasa horo da kuma shiryasu a zamanance.

Karamin ministan kimiyya da fasaha, Muhammed Abdullahi
Yan Najeriya Miliyan 85m Zasu Rasa Aikinsu, Inji Ministan Buhari Ya Fadi Dalili Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

A jawabin ministan yace:

"Yan Najeriya miliyan 85m na kan siraɗin rasa ayyukansu saboda rashin ilimin fasahar zamani da kuma kwarewa."

Kara karanta wannan

Osinbajo:Gwamnatin Buhari ta hada-kai da UNICEF, a koyawa mutum miliyan 20 neman na-kai

"A ma'aikatar mu muna amfani da tsarin horar wa kan fasahar zamani TVET domin shirya matasan mu su samu aikin yi, kuma a shirye muke mu haɗa kai da ƙungiyar UNICEF."

Akwai matsala a tsarin koyarwar jami'o'i

Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda yana cikin manyan baki a wurin taron, ya koka kan babban ƙalubale da ya maida matasa koma baya a ɓangaren ilimin fasaha da cewa ya samu asali ne tun daga tsarin koyarwar jami'o'in Najeriya.

Gwamnan ya ƙara da cewa manhajar da ake amfani da ita a manyan makarantun Najeria ya zama koma baya a cigaban da aka samu yanzun.

A cewarsa hakan ya sanya makarantun sun cigaba da yaye ɗalibai ba tare da kwarewar ilimin fasahar zamani ba.

Ganduje ya maida hankali kan lamarin

Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta ware kuɗi aƙalla miliyan N7m wajen gina cibiyoyin baiwa matasa horo kan sana'o'i da kwarewa kan fasahar zamani.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yi Watsi da Wata Bukatar Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

"Bincike ya nuna ta wannan hanyar ne kawai zamu maida matasan mu su zama masu dogaro da kansu," inji Ganduje.

A wani labarin kuma Kuna Yaudarar Kanku Ne, Jam'iyyar APC Ta Maida Martani Ga Gwamnonin PDP

Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa gamsuwa da mulkin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ne yake jawo hankalin gwamnonin PDP su sauya sheƙa zuwa APC, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Jam'iyya mai mulki tace wannan " Yaudarar kai ne" PDP ta cigaba da tsammanin cewa yayan ta zasu cigaba da zama a cikinta duk da gazawar da ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel