Babbar Magana: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dalibai Da Dama a Makarantar Sojoji
- Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da ɗaliban kwalejin sojojin ruwa dake Sepele, jihar Delta
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun kai wa motar bus ɗin ɗaliban hari har suka tafi da su
- Lamarin ya faru ne a jihar Edo yayin da ɗaliban ke kan hanyarsu ta komawa Sepele daga Kaduna
Sepele, Delta: Yan bindiga sun yi awon gaba da Dalibai dama a jihar Edo na kwalejin sojojin ruwa dake Sepele, Jihar Delta, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne ranar Litinin yayin da ɗaliban suke kan hanyarsu ta komawa Sepele daga jihar Kaduna.
Maharan sun farmaki motar Bas mai ɗaukar mutum 18 dake ɗauke da ɗaliban, inda suka tasa su zuwa wani wuri da ba'a sani ba.
Yan sanda sun kuɓutar da mutum 14
Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Edo, Kotongo Bello, ya tabbatar da lamarin ranar Laraba.
Yace ya zuwa yanzun rundunar yan sanda ta samu nasarar kubutar da ɗalibai 14 daga cikin waɗanda aka sace.
Bello ya ƙara da cewa a halin da ake ciki jami'an yan sanda na cigaba da binciken kwakwaf domin kubutar da ragowar ɗaliban.
"Mun samu nasarar kwato ɗalibai 14 daga ciki, kuma jami'ai na kan aikin bincike don gano inda ɓarayin suka yi da kuma kubutar da ragowar ɗaliban," inji shi.
Sai dai har yanzun hukumar kwalejin ba ta ce komai ba dangane da lamarin.
Wannan sharrin kan ɗaliban shine na baya-bayan nan da aka kai a faɗin ƙasar nan.
Wane hali ake ciki a Bethel Baptist Kaduna?
Mako uku da suka gabata wasu yan bindiga sun kutsa kai ɗakunan kwanan ɗalibai a makarantar Bethel Baptist Kaduna, inda suka sace guda 120.
A halim yanzun ɗalibai 38 sun kuɓuta daga hannun ɓarayin yayin da har yanzun dalibai 83 suke hannun yan bindigan.
A wani labarin kuma Labari Cikin Hotuna: Buratai Ya Gana da Shugaban Kasar Benin, Inda Ake Shari'ar Sunday Igboho
Jakadan Najeriya a Benin, Tukur Yusuf Buratai , ya gana da shugaban ƙasar, Patrice Talon, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Buratai ya gana da shugaban ne domin gabatar da kansa da takardar fara aikinsa a matsayin jakadan Najeriya a Benin.
Asali: Legit.ng