Da Duminsa: Yan Kasuwa sun Garkame Shagunansu a Aba Saboda Shari'ar Nnamdi Kanu

Da Duminsa: Yan Kasuwa sun Garkame Shagunansu a Aba Saboda Shari'ar Nnamdi Kanu

  • Yan kasuwa a cibiyar hada-hadar kasuwanci dake Aba sun kulle wurin kasuwancinsu saboda shari'ar Kanu
  • A yau Litinin ne za'a sake gurfanar da shugaban IPOB ɗin gaban mai shari'a Binta Nyako a Abuja
  • Ɗaya daga cikin yan kasuwan ya bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo

Yan kasuwa a cibiyar kasuwanci ta Aba dake jihar Abia sun dakatar da hada-hadar kasuwanci saboda shari'ar Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar tawaren IPOB, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Za'a cigaba da shari'ar shugaban ƙungiyar IPOB ɗin da safiyar Litinin ɗinnan da muke ciki a babbar kotu dake Abuja, wanda alkali Binta Nyako ke jagoranta, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Yan kaduwa sun dakatar da hada-hada a Aba
Da Duminsa: Yan Kasuwa Dun Garkame Shagunansu a Aba Saboda Shari'ar Nnamdi Kanu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kanu, wanda yake gaban kotu kan tuhumar cin amanar ƙasa, ya samu beli a shekarar 2017 bisa dalilin da ya shafi lafiyarsa.

An sake kamo shi ne a watan da ya gabata, kuma aka cigaba da tsare shi a ofishin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) bisa umarnin Kotu.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: El-Rufa'i Ya Dakatad da Komawa Makaranta a Jihar Kaduna Sai Baba Ta Gani

Rikici ka iya ɓarkewa

Ɗaya daga cikin yan kasuwan wurin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa manema labarai cewa ba su ɗauki wannan matakin ba don nuna goyon baya ga Nnamdi Kanu.

Yace: "Ba wai mun dakatar da hada-hadar mu bane don muna goyon bayan Nnamdi Kanu, mun ɗauki wannan matakin ne saboda abinda ka iya zuwa ya dawo na rikici a yankin yau."

Har a halin yanzun da muke kawo muku wannan rahoton ba'a kawo Nnamdi Kanu Kotun ba domin cigaba da shari'a kamar yadda aka tsara.

Hotunan Cibiyar Kasuwar Aba

An kulle shaguna a kasuwar Aba saboda shari'ar Kanu
Da Duminsa: Yan Kasuwa Dun Garkame Shagunansu a Aba Saboda Shari'ar Nnamdi Kanu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An dakatar da hada-hadar kasuwanci a Aba
Da Duminsa: Yan Kasuwa Dun Garkame Shagunansu a Aba Saboda Shari'ar Nnamdi Kanu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sake Sace Wani Basarake a Jihar Kaduna mako biyu bayan sace sarkin Kajuru

An sake yin awon gaba da basaraken garin Jaba, Kpop Ham na masarautar Jaba, jihar Kaduna, mai suna Jonathan Danladi Gyet Maude.

Sai dai har yanzun ba'a tabbatar da cewa basaraken shi kaɗai ya tafi gonar ko kuwa tare da masu tsaron shi ne.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yi Watsi da Wata Bukatar Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, shine ya tabbatar da sace basaraken ga manema labarai. Yace an sace Maude ne a yankin Panda, jihar Nasarawa yayin da ya kai ziyara domin duba gonarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262