Matsalar Tsaro: El-Rufa'i Ya Dakatad da Komawa Makaranta a Jihar Kaduna Sai Baba Ta Gani

Matsalar Tsaro: El-Rufa'i Ya Dakatad da Komawa Makaranta a Jihar Kaduna Sai Baba Ta Gani

  • Gwamnatin Kaduna ta dakatad da makarantu komawa daga hutun sallah har sai sun ji sanarwa
  • Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i yace an ɗauki wannan matakin ne domin baiwa sojoji damar yin aikinsu
  • A cewar gwamnan an kara turo sojoji jihar domin gudanar da aikin share yan bindiga baki ɗaya

Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da komawar ɗalibai makaranta daga hutun sallah a dukkan faɗin ƙananan hukumomin jihar har sai an ji sanarwa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Da yake jawabi a taron masu faɗa a ji, gwamna El-Rufa'i ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne saboda Operation ɗin da sojoji ke yi a kan yan bindiga a halin yanzu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Ya sanarwa mahalarta taron cewa na fara wannan aikin tankaɗe yan bindigan ne domin kawo ƙarshen aikin ta'addanci a jihar.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai
Matsalar Tsaro: El-Rufa'i Ya Dakatad da Komawa Makaranta a Jihar Kaduna Sai Baba Ta Gani Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Zamu kare rayuwar yan Kaduna

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnati zata yi duk mai yuwuwa domin kare 'ya'yan mazauna Kaduna daga harin yan bindiga.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An yi ram da Sowore yayin da ake ci gaba da shari'ar Nnamdi Kanu

Yace: "Rundunar soji ta kara turo mana jami'anta jihar Kaduna domin gudanar da wanna aiki, muna gargaɗin mutane da su kula da baƙin fuska domin yan ta'addan ka iya tserowa su saje a cikin Mutane."

A baiwa yan ƙasa lasisin rike makamai

A nashi jawabin, shugaban ƙungiyar likitoci reshen Kaduna, Dr Aliyu Sokomba, ya roƙi gwamnatin tarayya da ta bar wasu yan ƙasa su mallaki makamai don kare kansu.

Sakonba ya ƙara da cewa a halin da ake ciki yanzun ya zama wajibi a bar yan ƙasa su rike makamai saboda yawaitar sace mutane.

A cewarsa yan bindiga suna cin karen su babu babbaka a ɓangaren sace-sacen mutane cikinsu har da jami'an kiwon lafiya.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sake Aikewa da Sako Ga Iyayen Daliban Bethel Baptist Kaduna

Shugaban yan Baptist reshen jihar Kaduna, Ishaya Jangado, yace za'a sako ragowar daliban makarantar Bethel Baptist kashi-kashi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Kasuwa Sun Garkame Shagunansu a Aba Saboda Shari'ar Nnamdi Kanu

Ɓarayin sun aje 28 daga cikin ɗaliban a wani wuri kan hanyar Kaduna-Abuja ranar Asabar da daddare, inda jami'an sa kai JTF suka ɗauke su zuwa sansanin soji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262