Labari Cikin Hotuna: Buratai Ya Gana da Shugaban Kasar Benin, Inda Ake Shari'ar Sunday Igboho

Labari Cikin Hotuna: Buratai Ya Gana da Shugaban Kasar Benin, Inda Ake Shari'ar Sunday Igboho

  • Sabon jakadan Najeriya a ƙasar Benin, Tukur Yusuf Buratai, ya gana da shugaban ƙasar, Patrice Taron
  • Ganawar manyan mutanen biyo ta zo dai-dai lokacin da aka cafke ɗan fafutukar kafa kasar yarbawa, Igboho
  • An cafke Sunday Igboho ne a Kwatano yayin da yake kokarin tserewa zuwa kasar Germany

Jamhuriyar Benin: Jakadan Najeriya a Benin, Tukur Yusuf Buratai, ya gana da shugaban ƙasar, Patrice Talon, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Buratai ya gana da shugaban ne domin gabatar da kansa da takardar fara aikinsa a matsayin jakadan Najeriya a Benin.

Buratai da shugaban Benin
Labari Cikin Hotuna: Buratai Ya Gana da Shugaban Kasar Benin, Inda Ake Shari'ar Sunday Igboho Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A kwanakin baya shugaban ƙasa ya bayyana naɗa Buratai a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar jamhuriyar Benin, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ko Buratai ya yi maganar Igboho?

Ganawar Buratai da Talon tazo dai-dai lokacin da aka cafke shugaban yan tawaren yarbawa, Sunday Igboho, a ƙasar ta Benin.

Igboho, wanda aka kama a Kwatano yayin da yake kokarin tserewa zuwa ƙasar Germany.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Landan, inda zai kwashe makonni biyu

Shugaban yan fafutukar ya tsere ne daga Najeriya bayan jami'an tsaron farin kaya (DSS) sun kai hari inda yake zaune, daga baya kuma suka bayyana nemansa ruwa a jallo.

Hotunan Buratai tare da Taron, Shugaban Benin

Buratai ya gana da shugaban Benin
Labari Cikin Hotuna: Buratai Ya Gana da Shugaban Kasar Benin, Inda Ake Shari'ar Sunday Igboho Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Buratai da shugaban Benin, Talon
Labari Cikin Hotuna: Buratai Ya Gana da Shugaban Kasar Benin, Inda Ake Shari'ar Sunday Igboho Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani labarin kuma Kotu Ta Dage Sauraron Karar Sheikh Abduljabbar, Zai Cigaba da Zama a Gidan Gyaran Hali

Kotun shari'ar Musulunci dake Kofar Kudu ciki garin Kano, ranar Laraba, ta dage sauraron karar sheikh Abduljabbar Kabara har sai 18 ga watan Agusta, 2021.

Gwamnatin Kano ta shigar da ƙarar shehin malamin bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma wuce gona da iri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262