Ina bukatar miji, Budurwa mai son daidaituwar 'yancin mata da maza ta koka
- Bidiyon wata mata mai ra’ayin daidaita 'yancin maza da mata ya bayyana a Instagram tana rusa kuka
- Matar ta tabbatar wa da duniya cewa ta janye wannan ra’ayin nata kuma zata zage damtse wurin yi wa mijin da zai aureta biyayya
- Ta bayyana cewa yanzu dai bata da wani farashi kuma bata da zabi ko talaka ko mai kudi, gajere ko dogo koda kuwa mummuna ne babu komai
Ghana - Wata mata ‘yar kasar Kenya ta bayyana a wani bidiyo da aka wallafa a Instagram a shafi mai suna Instablog tana rusa kuka bayan kasuwa ta ci ta cinye amma ta kasa auruwa balle ta haihu.
Na sauya ra'ayi,miji nake nema
A bidiyon wanda aka wallafa a kafar sada zumunta ta Instagram ya nuna matar tana tallar kanta ko zata samu shiga ta zama matar aure. Ta bayyana takaici da kuncin da yanzu haka ya addabeta.
Matar wacce ba a bayyana sunanta ba ta ce ta tabbatar wa da duniya cewa ta canja ra’ayinta na rikau na daidaita ‘yancin maza da mata inda tace tabbas zata yi wa duk namijin da ya aureta biyayya.
KU KARANTA: Rimingado zai yi karar likitan da ya bashi shaidar asibiti ta bogi
Ina takaici idan na ga miji yana kulawa da matarsa
Shafin instablog9Ban damu da matsayin namiji ba, zan auraja ne suka wallafa wannan bidiyon sakamakon haka mutane suka yi ta tofa albarkacin bakinsu.
Kamar yadda matar tace tana matukar takaici idan taga miji yana kulawa da matarsa. Kamar yadda tace: “Na kasa auruwa balle in haihu kuma a halin da nake ciki gani nake yi kamar ni wata muguwa ce, ina takaici ganin masu aure suna jin dadi saboda mazansu basa kula wasu mata. Maza ababen so ne. Sai yanzu na fahimci cewa bazan iya rayuwa babu su ba.”
Ban damu da matsayin namiji ba, zan aura
Matar tace ko talaka ko mai kudi yazo za ta aure shi, koda kuwa gajerene ko dogo, a cewarta indai mutum ne mai rai tana sonshi.
Kamar yadda tace: “Ban damu ba ko talaka ne ko mai kudi, baki ko fari, gajere ko dogo, kyakkyawa ko mummuna duk ba matsala bane. Ni dai kawai ya kasance namiji mai rai don yanzu haka aure kawai nakeso."
KU KARANTA: Buhari ga 'yan siyasa: Kada ku yi amfani da ni wurin yaudarar masu saka kuri'a
A wani labari na daban, Sunday Adeyemo, mai rajin kwatar kasar Yarabawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya maka gwamnatin tarayya a kotu bisa kutsa mishi gida inda yake bukatar a biya shi naira biliyan 5.5.
Jami’an hukumar DSS sun kutsa gidan Igboho dake Ibadan a ranar 1 ga watan Yuli. Sakamakon hakan an kashe mutane 2 kuma an kama mutane 12 lokacin.
Kamar yadda TheCable ta ruwaito, Igboho ya ce yana cikin gidan shi a lokacin amma jami’an DSS basu gan shi ba.
Asali: Legit.ng