Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Sheikh Abduljabbar, Zai Cigaba da Zama a Gidan Gyaran Hali

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Sheikh Abduljabbar, Zai Cigaba da Zama a Gidan Gyaran Hali

  • Kotun musulunci ta dage sauraron karar sheikh Abduljabbar har sai watan Agusta
  • Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar shehin malamin ne bisa zarginsa da batanci ga Annabi
  • Rahotonni sun nuna cewa Abduljabbar ya yi kamar ba shi da lafiya, inda aka umarce shi ya zauna

Kotun shari'ar Musulunci dake Kofar Kudu ciki garin Kano, ranar Laraba, ta dage sauraron karar sheikh Abduljabbar Kabara har sai 18 ga watan Agusta, 2021, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnatin Kano ta shigar da ƙarar shehin malamin bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma wuce gona da iri.

Duk da cewa Abduljabbar ya musanta zargin da ake masa, Kotun bisa jagorancin alkali Ibrahim Sarki Yola, ya bada umarnin cigaba da tsare malamin a gidan yari.

An dage karar Abduljabbar
Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Sheikh Abduljabbar, Zai Cigaba da Zama a Gidan Gyaran Hali Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Meya jawo dage shari'ar?

A ranar Laraba da aka fara sauraron ƙarar, Mai gurfanar wa, Aisha Muhammad, ta roƙi kotun da ta ɗage shari'ar zuwa gaba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sheikh AbdulJabbar Kabara ya gurfana gaban kotun Shari'a

A cewarta, gwamnati na bukatar isasshen lokaci domin shiryawa shari'ar kuma ta gabatar da shaidun ta ga kotun.

"Muna bukatar isasshen lokacin domin shiryawa tare da gabatar da dukkan shaidun da muke da su ga kotu," inji Aisha.

Daman duk wannan lokacin gwamnati ba ta shirya ba?

Da yake martani kan bukatar masu kara, shugaban lauyoyin shehin malamin, Sale Bakaro, ya yi zargin cewa: "An garkame wanda muke karewa na tsawon kwanaki 12 amma abun takaici masu shigar da ƙara ba su shirya ba ɗuk tsawon wannan lokacin."

Bakaro yace hakan na nuna cewa akwai wata kulla-kulla na kara tsawaita shari'ar.

Lauyan Abduljabbar ya bukaci ɓangaren masu shigar da kara da su basu sunayen masu bada shaida, shaidu, da kuma inda suka samo shaidun.

Hakanan kuma Lauyan ya bukaci a ba shi takaitaccen jawabi da kuma kwafin firar da wanda yake karewa ya yi da yan sanda.

Kara karanta wannan

Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba

Lauyan ya kuma bukaci a rinka basu rikodin ɗin murya, bidiyo, hoto ko wasu takaddu da ake zargin malamin yayi batanci kafin kowane zaman kotu kamar yadda doka ta tanazar.

Ya zaman shari'ar ya kasance

Mai gabatar da kara ta nemi kotu ta dage sauraron shari'ar zuwa 25 ga watan Agusta yayin da mai kare wanda ake ƙara ya nemi a dage ta zuwa 11 ga watan Agusta.

Alkali Yola ya bayyana ɗage karar zuwa 18 ga watan Agusta, sannan ya bada umarnin a cigaba da tsare Malam Abduljabbar a gidan gyaran hali.

Rahotanni sun bayyana cewa Abduljabbar ya yi kamar mara lafiya inda aka umarceshi da ya zauna biyo bayan neman bukatar hakan da lauyansa yayi.

A wani labarin kuma Ruwan Sama Mai Tsanani Ya Lakume Rayuwar Mutum Biyu da Gidaje 1,500 a Jihar Katsina

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kastina (SEMA) ta bayyana cewa ruwan sama ya hallaka mutum 2 a Katsina.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Hukumar tace sama da gidaje 1,500 ne suka salwanta sanadiyyar ruwan saman a kananan hukumomi uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel