Da duminsa: Sheikh AbdulJabbar Kabara ya gurfana gaban kotun Shari'a

Da duminsa: Sheikh AbdulJabbar Kabara ya gurfana gaban kotun Shari'a

  • Tun bayan kamashi, Malam AbdulJabbar ya bayyana a kotu karon farko
  • An gurfanar da shi a kotun Shari'a dake cikin jihar Kano
  • Ana tuhumarsa da laifin batanci da manzon Allah

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Malami, Sheikh AbdulJabbar Nasir Kabara gaban kotun Shari'ar Musulunci a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, 2021.

Wannan ya biyo bayan damkeshi da hukumar yan sanda tayi gabanin bikin Sallar Layya a ranar 17 ga Yuli, 2021.

A hotunan da BBC Hausa ta dauka, an ga AbduJabbar zaune cikin kotun tare da jam'ian gidajen gyara hali.

Da duminsa: Sheikh AbdulJabbar Kabara ya gurfana gaban kotun Shari'a
Da duminsa: Sheikh AbdulJabbar Kabara ya gurfana gaban kotun Shari'a Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Dalilin da yasa aka kama Sheikh AbdulJabbar?

Gwamnati ta kame Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara bisa laifin batanci ga manzon Allah SAW.

Kwamishina na yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta nuna cewa hakan ya biyo bayan karbar rahoton farko da aka yi daga ofishin ‘yan sanda daga Ofishin Babban Lauya da kuma kwamishinan shari’a wanda ya shirya tuhuma kan malamin.

Kara karanta wannan

Darajar Naira ta fadi bayan sanarwan CBN na daina sayarwa yan kasuwar canji Dalar Amurka

Karo na farko, Ganduje ya yi magana kan lamarin AbdulJabbar Kabara

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a karon farko ya yi furuci kan lamarin Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara wanda Malaman Kano suka kai kara wajensa.

Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta bibiyi lamarin har zuwa karshe.

Ganduje ya bayyana hakan ne a jawabin da lokacin da ya kai ziyarar Barka da Sallah gidan Qadiriyya, Kabara domin yiwa Shugaban Darikar Qadiriyya na Africa Sheikh Qaribullahi Sheikh Nasiru Kabara gaisuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel