Ruwan Sama Mai Tsanani Ya Lakume Rayuwar Mutum Biyu da Gidaje 1,500 a Jihar Katsina

Ruwan Sama Mai Tsanani Ya Lakume Rayuwar Mutum Biyu da Gidaje 1,500 a Jihar Katsina

  • Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kastina (SEMA) ta bayyana cewa ruwan sama ya hallaka mutum 2 a Katsina
  • Hukumar tace sama da gidaje 1,500 ne suka salwanta sanadiyyar ruwan saman a kananan hukumomi uku
  • Ruwan saman wanda ya ɗauki tsawon lokaci ana yinsa ya cika manyan hanyoyin cikin birnin Katsina

Katsina:- Hukumar agajin gaggawa ta jihar Katsina (SEMA) tace sama da gidaje 1,500 ne suka salwanta sanadiyyar ruwan sama mai tsanani ranar Litinin.

Kakakin hukumar SEMA, Umar Muhammed, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a kananan hukumomi uku dake jihar, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Mr. Muhammed ya shaidawa hukumar dillancin labaran Najeriya (NAN) ranar Laraba cewa daga cikin adadin an samu gidaje 800 da abun ya shafa a Faskari.

Yayin da abun ya shafi gidaje 400 a ƙaramar hukumar Bindawa da kuma gidaje 300 a Sabuwa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

Ruwan sama ya cika hanyoyi a Katsina
Ruwan Sama Mai Tsanani Ya Lakume Rayuwar Mutum Biyu da Gidaje 1,500 a Jihar Katsina Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhammed ya kara da cewa matsanancin ruwan saman wanda ya ɗauki aƙalla awa 5 a Bindiga ya kashe mutum biyu.

Rahotanni sun nuna cewa an fara ruwan saman ne tun karfe 10:00 na safiyar ranar Litinin sannan ya tsaya da karfe 4:00 na yamma, inda ruwa ya tilastawa direbobi barin motocin su.

Me mutanen Kastina ke cewa kan ruwan saman?

Wasu daga cikin mazauna kwaryar birnin Katsina sun koka kan yadda ambaliyar ruwa ta lalata manyan hanyoyin cikin gari.

Mafi yawancin direbobin dake bin hanyar Kofar Kaura da wasu saassan yankuna a cikin birnin dole tasa suka koma amfani da hannu ɗaya.

Wani direba, Muhammad Safana, ya bayyana halin da hanyoyin ke ciki a matsayin abun damuwa, yace yanayin ka iya fin haka lalacewa idan aka cigaba da yin irin wannan ruwan saman.

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

Yace: "Kamar yadda kuka gani ruwan sama ne ya haddasa ambaliya, wanda ya cika manyan hanyoyin cikin gari, kuma ya taɓa wasu gidaje."

"Yayin da nake wucewa ta Tudun Katsira, ambaliyar ta shafi gidaje sosai saboda rashin kyawawan hanyar ruwa."

A wani labarin kuma El-Rufa'i Ya Dakatad da Komawa Makaranta a Jihar Kaduna Sai Baba Ta Gani

Gwamnatin Kaduna ta dakatad da makarantu komawa daga hutun sallah har sai sun ji sanarwa.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i yace an ɗauki wannan matakin ne domin baiwa sojoji damar yin aikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262