Ni dai jam'iyyar APC haihata-haihata har abada, Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal

Ni dai jam'iyyar APC haihata-haihata har abada, Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana rashin gamsuwarsa da mulkin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) inda yace Allah ya kiyaye ya koma APC.

Gwamnan ya caccaki gwamnatin tarayya kan yadda take mulkan yan Najeriya kuma ta jefa yan kasa cikin kunci da talauci.

Tambuwal wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya bayyana hakan ne yayin taron da gwamnonin jam'iyyar adawa suka yi a jihar Bauchi, rahoton Tribune.

Ya yi Alla-wadai da irin salom mulkin APC "da ya jefa yan Najeriya cikin halin kunci, bakar talauci da rashin kayan jin dadin rayuwa."

"Allah ya kiyaye in koma APC ta kowani dalili."

Ni dai jam'iyyar APC haihata-haihata har abada, Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal
Ni dai jam'iyyar APC haihata-haihata har abada, Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal
Asali: Twitter

Yayin magana ranar Litnin da yake jagorantar sauran gwamnonin PDP wajen kaddamar da sabon fadar gwamnatin Bauchi da gwamna Bala Mohammed ya gina, Tambuwal yace yan Najeriya na kuka karkashin mulkin APC.

Yace dukkan gwamnonin PDP na kokari a jihohinsu kuma ya yi kira ga yan Najeriya su tayasu da addu'a.

Kara karanta wannan

Ba Bu Wanda Zai Tsoratar Da Mu Domin Mu Shiga APC, Gwamnonin PDP

Yace:

"Dukkan gwamnoninmu na kokari da ikon Allah. Muna bukatan addu'o'inku da kuma gwamnatin tarayya, saboda idan ba tayi aiki ba dukkanmu zai shafa. Kuma yanzu ma abin na shafenmu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel