An gagara dinke barakar da ta shiga PDP duk da Gwamna ya zauna da Wike, Secondus

An gagara dinke barakar da ta shiga PDP duk da Gwamna ya zauna da Wike, Secondus

  • Prince Uche Secondus ya na so ya zarce a matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP
  • Gwamnan Ribas, Nyesome Wike, da wasu su na so ayi waje da Uche Secondus
  • Ana kokarin ayi sulhu, Gwamnan jihar Ribas ya musanya rade-radin sabani

The Nation ta rahoto cewa akwai baraka a gidan jam’iyyar PDP saboda sabanin da aka samu tsakanin Prince Uche Secondus da gwamna Nyesom Wike.

Gwamnoni suna neman yi wa Majalisar NWC taron dangi

Shugaban jam’iyyar hamayyar ya samu matsala da gwamnan da ya kawo shi a 2017, inda gwamnan yake neman hana Uche Secondus damar tazarce.

Jaridar ta ce wannan sabani zai iya yin tasiri a zaben shugabannin da za a yi a karshen shekarar nan.

Kamar yadda binciken da aka yi ya nuna, wasu manyan gwamnonin PDP suna tare da Nyesom Wike wajen hana Secondus cigaba da zama shugaban PDP.

Ana kokarin sasanta Nyesom Wike da Uche Secondus

Amma na-kusa da shugaban jam’iyyar adawar na kasa suna ganin ya kamata a kyale shi ya cigaba da jagorantar PDP saboda irin gaskiya da rikon amanarsa.

Wannan matsalar ce ta jawo gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya zauna da Nyesom Wike da Uche Secondus kwanaki domin a sasanta sabanin da suka samu.

Rahoton ya bayyana cewa gwamna Ortom bai iya dinke barakar da ta yi wa jam’yyar ta PDP katutu ba, a haka aka tashi taron a Makurdi ba tare da an dace ba.

'Yan PDP
Shugabannin PDP Hoto: freedomonline.com.ng
Asali: UGC

Abin da ake tunanin ya jawo wannan rikicin cikin-gida

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa sabanin Secondus da Wike ya samo asali ne a lokacin da aka yi zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a 2018.

“Dadaddiyar rigimar 2018 ce, Secondus ya ki yarda ya yi abin da gwamna Wike yake so. Aminu Tambuwal ya sha kashi a hannun Atiku Abubakar.”

Sai dai Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya nuna sam babu wata rigima tsakaninsa da Uche Secondus.

A APC kuma, za a ji cewa daya daga cikin wadanda su ka kafa jam'iyyar ya bada satar amsa kan zaben 2023, ya fadi wanda yake ganin zai samu tikiti a 2023.

Osita Okechukwu ya ce akwai yiwuwar tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu ne zai rike wa jam'iyyar APC mai mulki tuta a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel