Sojoji sun garkame kasuwannin jihar kudu saboda nuna goyo baya ga Nnamdi Kanu

Sojoji sun garkame kasuwannin jihar kudu saboda nuna goyo baya ga Nnamdi Kanu

  • Sojoji a jihar Imo sun hana wasu 'yan kasuwa bude shagunansu saboda nuna goyon baya ga Nnamdi Kanu
  • Lamarin ya faru ne a yau Talata, 27 ga watan Yuli, 2021 yayin da sojojin suka garkame kasuwar
  • Sai dai, kakakin rundunar ta sojin yankin ya ce bai ji labarin faruwar hakan ba kwata-kwata

Jihar Imo - Sojoji a ranar Talata sun hana ‘yan kasuwa a kasuwannin katako da na kayayyakin gini a Orlu, jihar Imo, budewa domin gudanar da kasuwancinsu na ranar.

Mafi yawan ‘yan kasuwar a kasuwannin biyu a ranar Litinin din da ta gabata sun ki bude shagunansu don nuna goyon baya ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar tuhumar ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Sojojin, wadanda ke gudanar da aikin shingen binciken ababen hawa kusa da manyan kasuwannin biyu a Orlu, sun hana ‘yan kasuwar bude shagunansu da duk wata harkar kasuwanci.

Kara karanta wannan

Kotu ta hana Gwamnatin Buhari aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki

Sojojin sun garkame kasuwar wata jihar kudu saboda Nnamdi Kanu
Shugaban awaren yankin kudu maso gabas, Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

'Yan kasuwar sun shaida wa wakilin jaridar Punch cewa sojoji sun umarci masu gadin kasuwarda kada su bude kofofin kasuwannin.

Yayin da sojoji suka ci gaba da aikinsu na tsayawa da bincike a gaban kasuwannin biyu, ‘yan kasuwar da suka zo tun da misalin karfe 7 na safe sun ga kofar kasuwannin a garkame.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar ya shaida wa jaridar Punch cewa bai samu damar zuwa shagonsa ba a ranar Talata lokacin da ya zo don cin kasuwar ranar.

Dan kasuwar, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya ce:

"Jiya, kusan kowa bai bude shago ba don nuna goyon ga Nnamdi Kanu. Kamar yadda muka zo yau, sojoji sun hana mu bude kasuwannin biyu.
"Ba mu ma shiga kasuwanni ba saboda kofofofin kasuwannin kayan ginin da na katako suna kulle. Sojojin sun gaya mana cewa ba za a bar mu mu bude shago ba har sai wani lokaci.”

Kara karanta wannan

Dillalan shanu na neman filin kiwo mai girman murabba'in mita 30000 a wata jihar kudu

Shugaban kasuwannin, Emmanuel Ibegbulem, wanda ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho, ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta jihar.

Kakakin rundunar 34 Artillery Brigade Command, Obinze Owerri, Babatude Zubiruo, lokacin da aka tuntube shi, ya ce shi bai san da labarin ba.

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Akwai yiwuwar Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, dake fuskantar manyan laifuka da hukuncinsu ya kai ga hukuncin kisa ko daurin rai da rai yayin da za a ci gaba da shari’arsa a yau Litinin, 26 ga watan Yuli.

Gwamnatin tarayya a cikin wata wasika da ta aika wa jami’an diflomasiyyar kasashen yamma ta zargi shugaban na IPOB da aiwatar da kashe-kashen jama’a a kasar.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin ta ce Kanu ya shirya kisan mutane akalla 60 da lalata dukiyoyi a wasu hare-hare 55 da aka kai hari a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu cikin watanni hudu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudi N982Bn, karin kan na 2021

Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu zuwa wani lokaci, zai ci gaba da zama a DSS

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta dage shari’ar Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar tsageru IPOB saboda gazawar Gwamnatin Najeriya na gurfanar da shi a gaban kotu ranar Litinin, in ji Channels Tv.

Lokacin da aka dago batun, lauya mai gabatar da kara, M. B. Abubakar, ya sanar da kotu cewa an shirya sauraren karar kuma a shirye suke su ci gaba.

Amma lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor, ya sanar da kotu cewa akwai karar da ake jira a gaban kotu don a sauya Kanu daga tsarewar hukumar DSS zuwa cibiyar gyaran hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags:
Online view pixel