Labari Da Ɗuminsa: An Sace Sojojin Ruwan Nigeria Su Bakwai a Edo

Labari Da Ɗuminsa: An Sace Sojojin Ruwan Nigeria Su Bakwai a Edo

  • Masu garkuwa a mutane sun sace sojojin ruwan Nigeria bakwai a jihar Edo
  • Jami'an Yan sanda a jihar Edo sun yi nasarar ceto biyar daga cikinsu
  • Sojojin ruwan sun taso daga Kaduna ne suna hanyar zuwa jihar Delta

Rahoton da Daily Trust ta wallafa na cewa an sace dakarun sojoji ruwan Nigeria bakwai a jihar Edo.

An sace jami'an tsaron ne yayin da suke kan hanyarsu na zuwa Delta daga Kaduna.

Labari Da Ɗuminsa: An Sace Sojojin Ruwan Nigeria Su Bakwai a Edo
Labari Da Ɗuminsa: An Sace Sojojin Ruwan Nigeria Su Bakwai a Edo
Asali: Original

Daily Trust ta gano cewa yan sanda sun ceto biyar daga cikin sojojin ruwan.

An bayyana cewa sojojin ruwan da suka taso daga sansanin sojojin ruwa ta Kaduna ne a hanyar Sapele zuwa Warri.

A cewar majiya:

"Suna kan hanyarsu ne na zauwa kwalleji koyan aikin Injiniya da ke Sapele, jihar Delta."

An gano cewa jami'an yan sandan Nigeria na jihar Edo, bayan samun bayyanan sirri su ceto biyar daga cikin sojojin yayin da sauran biyun har yanzu ba a gano su ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Boko Haram sun saki hotunan sojoji da jami'an da suka yi garkuwa da su a Yobe

Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Kotongs Bello ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai yi cikaken bayani ba.

Ya ce:

"Mun ceto biyar, sauran biyu har yanzu ba a ceto su ba. Wannan shine abin da na sani."

A baya-bayan nan dai ana fama da kallubalen rashin tsaro a sassan Nigeria kuma abin har jami'an tsaro ya shafa.

Kungiyar ta'addanci na ISWAP, a baya bayan nan ta fitar da hotunan wasu sojoji da ta ce ta kama a jihar Yobe.

'Yan Fashi Da Makami Sun Bindige Manjo Na Soja Har Lahira A Jigawa

Rundunar sojojin Nigeria ta bayyana cewa ƴan fashi da makami sun bindige muƙadasshin kwamandan 196 Battalion, Manjo MS Sama'ila a Dundubus, Jigawa, News Wire ta ruwaito.

A cewar sanarwar da rundunar sojojin ta fitar a ranar Talata, an kashe Sama'ila ne misalin ƙarfe 11.30 na daren ranar Lahadi a hanyarsa ta zuwa Kano daga Maiduguri da mai tsaronsa Alisu Aliyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

Yayin da an kai gawar Sama'ila asibitin ƙwararru ta Rashid Shekoni da ke Dutse, Aliyu wanda ya tsira da harbin bindiga yana samun kulawa a asibitin na Shekoni da ke Dutse kamar yadda News Wire ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel