Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudi N982Bn, karin kan na 2021
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya sanya hannu kan sabon kari a kasafin kudin 2021
- Shugaban ya rattaba hannun ne a yau Litinin, 26 ga watan Yuli a fadarsa dake babbar birnin tarayya Abuja
- Shugaban ya rattaba hannun a gaban wasu manyan jiga-jigan gwamnati da masu ruwa da tsaki a kasar
Shugaban kasar Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari (Mai ritaya) ya rattaba hannu kan kasafin kudin da ya kai N982.7bn, kari kan na shekarar bana ta 2021 domin warware wasu matsaloli da kasar ke fuskanta.
Wannan ya fito ne daga wata sanarwa mai magana yawun shugaban kasa , Garba Shehu ya fitar a yau Litinin 26 ga watan Yuli, 2021, wacce Legit,ng Hausa ta samo.
Sanarwar ta bayyana cewa, karin kasafin kudin za a yi amfani dasu ne wajen warware matsalolin tsaro da kuma annobar Korona da kasar ke fuskanta.
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin a Abuja ya rattaba hannu kan karin kasafin kudi na N982.7bn na 2021 don magance matsalar tsaro cikin gaggawa da bukatun Korona na kasar.
Shugaba Buhari ya rattaba hannun ne kan dokar karin kasafin kudi, 2021 a gaban wasu jiga-jigan gwamnati da makusantansa a mulki a fadarsa dake Abuja, wadanda suka hada da:
- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo
- Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha
- Shugaban Ma'aikata, Farfesa Ibrahim Gambari
- Darakta-janar na kasafin kudi, ofishin tarayya, Ben Akabueze
- Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan al'amuran majalisar kasa (Gida), Hon Umar el-Yakub
Yadda kasafin zai yi aiki
Sanarwar, ta bayyana yadda wasu daga cikin kudaden za su tafi a wasu ayyukan da gwamnatin tarayya ta sa a gaba.
A cewar sanarwar:
"Daga cikin kudin, N123.3m ne na amfanin yau da kullum (ba-bashi ba) yayin da jimlar N859.3bn su ne na bayar da gudummawa ga Asusun Raya Kasa da za a ke kashewa har shekarar ta kare a ranar 31 ga Disamba, 2021."
Hakazalika, sanarwar ta ce, shugaba Buhari ya yaba wa majalisar dokoki ta kasa wajen namijin kokari na tabbatarwa da amincewa da bukatar karin kasafin.
"Shugaba Buhari ya yaba wa Majalisar Dokoki ta kasa kan gaggauta dubawa da amincewa da karin kasafin, yana mai bayar da tabbacin cewa bangaren zartarwa na gwamnati za su tabbatar da isar da manyan ayyuka a kan kari don cimma burikan da ke cikin kasafin.
Jan Aiki: Shugaba Buhari zai gina manyan gidajen yari guda 3 a Kano da wasu jihohi
A wani labarin, Gwamnatin Tarayya za ta gina sabbin cibiyoyi guda uku wadanda za su iya rage cunkoso na gidajen gyaran hali a kasar, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a 23 ga watan Yulin 2021 a wajen bikin kaddamar da Hukumar Kula da Fursunoni ta Najeriya, da ke Hedikwatar rundunar ta Jihar Osun, a Osogbo.
Mista Aregbesola ya ce za a gina sabbin wuraren ne a Karchi ta Abuja, Kano, da Bori a jihar Ribas.
Asali: Legit.ng