Na'uarar CCTV ta nuna yadda yar shekara 9 ta haddasa gobarar katafaren kantin Prince Ebeano a Abuja

Na'uarar CCTV ta nuna yadda yar shekara 9 ta haddasa gobarar katafaren kantin Prince Ebeano a Abuja

  • Bayan kimain mako guda da aukuwar gobarar, na'urar CCTV ta bayyana abinda ya faru
  • Ashe wata yarinya ce ta kunna wuta da gayya cikin kantin
  • Gaba daya kantin ya kone kurmus kuma dukiyar kimanin N5bn akayi asara

FCT Abuja - Faifan bidiyon da na'urar CCTV ta nada ya nuna yadda 'yar yarinya mai shekara 9 da haihuwa ta haddasa gobara a katafaren kantin Prince Ebeano dake unguwar Lokogoma, birni tarayya Abuja.

Bidiyon wanda ya yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya nuna yadda yarinyar ta kunna wutan Leta a wuraren daka ajiye tukunyar gas cikin kantin.

Kakakin hukumar kwana-kwanan birnin tarayya, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa sassan hukumar daban-daban irin Nji, Garki, Asokoro sun yi yakin kashe wutar amma abin yaci tura.

A bidiyon da Legit ta gani ranar Lahadi, yarinyar wacce ba'a gano sunanta ba har yanzu ta shiga cikin kantin tare da wasu mata biyu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sarakunan Yarbawa sun gana a jamhuriyar Benin kan batun Sunday Igboho

Na'uarar CCTV ta nuna yadda yar shekara 9 ta haddasa gobarar katafaren kantin Prince Ebeano a Abuja
Na'uarar CCTV ta nuna yadda yar shekara 9 ta haddasa gobarar katafaren kantin Prince Ebeano a Abuja Hoto: Prince Ebeano
Asali: UGC

Yarinyar sanye da bakar riga da wando ta tafi kai tsaye wurin da aka ajiye tukunyar gas da Leta. Daga bisani ta dauki Leta daya ta kuna kan sauran kuma tayi wucewarta.

Bayan wutar ta kama kanti bal-bal, na'urar ta nadi yarinyar a waje tare wata mata tana dariya.

Amma a wani faifan bidiyon, an ga yadda aka damke yarinyar da matar kuma suna shan tambayoyi.

Shin ka ga bidiyon?:

Gobara ta yi kaca-kaca da wani shahararren shagon siyayya a Abuja

Legit ta kawo muku rahoton Shahararren Shagon Siyayya na Prince Ebeano da ke gundumar Lokogoma a babban birnin tarayya Abuja ya kone da yammacin ranar Asabar.

Wani shaidar gani da ido ya ce jami’an kashe gobara sun isa wurin kuma sun yikokarin kashe wutar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel