Yan Bindigan da Suka Sace Basaraken Gargajiya Mai Daraja Ta Daya a Kaduna Sun Kira Iyalansa Ta Wayar Salula

Yan Bindigan da Suka Sace Basaraken Gargajiya Mai Daraja Ta Daya a Kaduna Sun Kira Iyalansa Ta Wayar Salula

  • Ɓarayin da suka yi awon gaba da basaraken gargajiya lamba ɗaya a Kaduna sun kira iyalansa a waya
  • Masu garkuwan sun nemi a tattara musu kuɗi naira miliyan N100m a matsayin na fansar basaraken
  • Rahoto ya nuna cewa an yi awon gaba da Maude, basaraken Jaba, a wani yankin jihar Nasarawa

Jaba, Kaduna:- Yan bindigan da suka sace basarake mai muhimmanci a masarautar Jaba, Kpop Ham, Gyet Maude, sun tuntubi makusantansa.

Ɓarayin sun kira iyalansa ta wayar salula, inda suka nemi a biya su kuɗin fansa har naira miliyan N100m, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa, wata majiya tace ɓarayin sun nemi kuɗin fansa ne yayin da suka kira ɗaya daga cikin iyalan basaraken ranar Talata.

Yan Bindigan da Suka Sace Basaraken Kaduna sun nemi kuɗin fansa
Yan Bindigan da Suka Sace Basaraken Gargajiya Mai Daraja Ta Daya a Kaduna Sun Kira Iyalansa Ta Wayar Salula Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Majiyar tace: "Sun kira iyalansa a waya ranar Talata, kuma sun nemi kuɗin fansa miliyan N100."

Basarake da yafi daɗewa a arewa: Shi kaɗai aka sace?

Kara karanta wannan

Dattijon da Yaje Kai Kudin Fansa Miliyan N30m Ya Kubuta, Ya Fadi Halin da Daliban Islamiyyar Tegina Ke Ciki

Basaraken Jaba, Maude, shine wanda ake ganin yafi kowane basaraken gargajiya daɗewa a arewacin Najeriya.

Yan bindiga sun sace Maude ne ranar litinin da misalin ƙarfe 2:00 na rana yayin da yaje gonarsa dake yankin Gitata, jihar Nasarawa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Legit.ng hausa ta gano cewa yankin Gitata yana kusa da iyakar jihar Kaduna da kuma jihar Nasarawa.

Rahotanni sun bayyana cewa basaraken gargajiyan ɗan kimanin shekara 83, ya fita ne tare da direbansa da kuma masu tsaron shi.

Amma wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwan sun kyale direban da kuma masu tsaronsa yayin da suka tafi da basaraken zuwa daji.

A wani labarin kuma Dattijon da Yaje Kai Kudin Fansa Miliyan N30m Ya Kubuta, Ya Fadi Halin da Daliban Islamiyyar Tegina Ke Ciki

Mutumin da yaje kai kuɗin fansa ga ɓarayin da suka sace ɗaliban islamiyyar Tegina, jihar Neja ya kuɓuta daga hannunsu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sake Sace Wani Basarake a Jihar Kaduna

Kasimu Barangana ya shaidawa premium times bayan an sako shi ranar Litinin cewa ɓarayin sun aje ɗalibai a wurare 25 cikin yanayi mara dadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel